Ban damu da wanda zai gaje ni ba a 2023 – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai damu da wanda zai gaje shi ba a matsayin shugaban ƙasa saboda “ya ajiye rahoton komai da komai”.

Shugaban ya faɗi hakan ne a hirarsa da kafar talabijin ta Channels TV a yammacin Laraba, yana mai cewa “zaɓen 2023 ba matsalata ba ce”.

“Ban damu da wanda zai gaje ni ba, rabu da shi ya zo ko ma wane ne,” in ji shi.

Da yake amsa tambaya kan ko me ke zuwa masa a rai idan ya ji an ambaci zaɓen 2023, Buhari ya amsa da cewa: “Ba matsalata ba ce.”

Da aka tambaye shi: “Ba ka damu game da wanda zai gaje ka ba? Sai ya ce:

“Bar shi ya zo ko ma wane ne. Na tabbata na ajiye rahoton duk wani abu mai muhimmanci. Bai kamata wani ya kira ni ba da shaida a gaban kotu ba a kan wani abu, idan ba haka ba kuma zai shiga matsala.”

Buhari ya ce duk da cewa ba shi da wani ɗan takara da yake goyon baya a jam’iyyarsu ta APC mai mulki ya gaje shi amma idan ya bayyana shi za a iya halaka shi.

“A’a, saboda idan na faɗa za a iya kawar da shi. Gara na bar shi a sirrance,” a cewarsa.

‘Mun ayyana ‘yan fashin daji ‘yan ta’adda saboda abin da suka sani kenan’

Buhari ya amsa tambayoyi kan batutuwa da dama yayin hirar da aka naɗa a fadarsa ta Aso Rock Villa, ciki har da matsalar ‘yan fashin daji na arewa maso yamma.

“Mun ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda…saboda shi ne kaɗai abin da za su fahimta,” a cewarsa.

Sai dai babu wata sanarwa da ta nuna cewa gwamnatin ta ayyana su ‘yan ta’adda a hukumance tun bayan da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya nemi kotu ta ba su damar yin hakan duk da cewa kotun ta amince da buƙatar gwamnatin.

‘Ba za mu saki Nnamdi Kanu ba’

‘Yan makonni bayan alƙawarin da ya yi wa dattawan al’ummar Ibo na duba yiwuwar sakin ɗan tawaye Nnamdi Kanu, Buhari ya ce “ba za mu iya sakin sa ba”.

Ya ce: “Akwai sashen da ba zan iya taɓawa ba, shi ne na shari’a. Batun Kanu yana gaban kotu. Amma abin mamakin shi ne, lokacin da yake Turai yana zagin wannan gwamnati, na zaci zai so ya zo ya kare kansa daga waɗan nan zagr-zargen.

“Saboda haka muna ba shi dama ce ta kare kan sa bisa tsarinmu, ba wai ya koma Turai ya ci gaba da zaginmu ba kamar ba ɗan Najeriya ba. Ya zo nan ya soke mu…waɗanda ke cewa ya kamata a sake shi, a’a, ba zamu iya sakin sa ba.”

A watan Nuwamba ne dattawan suka gana da Buhari a Abuja, inda suka nemi ya tausaya wa jagoran na haramtacciyar ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da ke neman kafa ƙasar Biafra a kudu maso gabashin Najeriya.

Ba na goyon bayan zaɓen ‘yar tinƙe – Buhari

Shugaban ya ce ba ya goyon bayan tsarin zaɓe na ‘yar tinƙe yayin zaɓen ‘yan takara a cikin jam’iyyun siyasa, wanda sabuwar dokar zaɓe ta tanada.

Buhari ya ce ya kamata a bai wa ‘yan Najeriya zaɓi uku, ba wai ‘yar tinke kawai ba.

“Abin da nake cewa shi ne, ba zai yiwu ka taƙaita zaɓin al’umma ba a kan abu ɗaya kawai kuma ka ce dimokuraɗiyya kake yi. Dole ne a ba su ‘yancin zaɓi uku,” in ji shi.

A cewarsa: “Akwai ‘yar tinƙe da jefa ƙuri’a da kuma masalaha.”

Bai kamata a ƙirƙiri ‘yan sandan jihohi ba – Buhari

Shugaba Buhari ya ce “babu maganar ƙirƙirar ‘yan sandan jihohi” yayin da yake maganar rikicin makiyaya da manoma.

Shugaban ya kamanta ƙirƙirar ‘yan sandan jihohi da kuma alaƙa tsakanin ƙananan hukumomi da gwamnatin jihohinsu.

Ya ce: “Ko a yanzu kun ga gwamnatocin jiha na bai wa ƙananan hukumomi haƙƙinsu?”

More from this stream

Recomended