Abin da ya kamata ku sani kan wasan Man United da Man City

Solskjaer Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Asabar za a buga wasan hamayya tsakanin Manchester United da Manchester City a gasar Premier League a Old Trafford.

Manchester City tana ta uku a kan teburin Premier League da maki 20, ita kuwa Man United tana ta biyar da makinta 17.

Kungiyoyin sun kara sau uku a 2020/2021 da yin wasa biyu a Premier League da karawa a FA Cup.

Sun fara wasa ranar 12 ga watan Disambar 2020, inda suka tashi 0-0 a gidan United.

Sai kuma suka hadu a karawar FA Cup ranar 6 ga watan Janairun 2021, inda City ta yi nasara da ci 2-0.

A fafatawar Premier karo na biyu a kakar, United ta yi nasara da ci 2-0 a Etihad ranar 7 ga watan Maris din 2021.

United ba ta yi rashin nasara ba a wasa hudu kwanan nan a tsakaninsu a Lik, wadda ta ci wasa uku da canjaras daya.

Wasa uku kungiyar da ke gida ta yi nasara daga 16 da suka fafata a dukkan karawa a baya.

City na fatan cin wasa na takwas a gidan United, wadda ta ci shida da canjaras biyu da rashin nasara a karawa biyu

More from this stream

Recomended