[BBC Hausa]: Juventus za ta sayar da Ramsey, Chelsea za ta rabu da Kante

Aaron Ramsey

Asalin hoton, OTHERS

Juventus na shirin sayar da dan wasanta na tsakiya dan Wales Aaron Ramsey, mai shekara 30 a watan Janairu, inda West Ham da Everton da Newcastle suke sha’awarsa. (Sun)

Asalin hoton, Getty Images

Inter Milan ta sa mai tsaron ragar Arsenal da Jamus Bernd Leno, mai shekara 29, a cikin jerin ‘yan wasan da take son saya. (Fichajes)

Asalin hoton, Getty Images

Tottenham na son zawarcin dan wasan tsakiya na Juventus da Sweden Dejan Kulusevski mai shekara 21. (Mirror)

A shirye Chelsea take ta sayar da dan wasanta na tsakiya dan Faransa N’Golo Kante mai shekara 30 a bazara mai zuwa. (Fichajes)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Tun 2016 N’Golo Kante yake Chelsea

Chelsea na shirin sabon tayi a kan dan wasan gaba na gefe na Italiya Federico Chiesa. Mai shekara 23 wanda ke zaman aro a Juventus daga Fiorentina, akwai damar Juventus ta saye shi ya zauna dindindin. (Calciomercato)

Real Madrid ta sanya ido kan dan bayan Leicester City da Turkiyya Caglar Soyuncu, mai shekara 25, wanda idan ya yi mata za ta nemi sayensa. (DefensaCentral)

West Ham na son sayen dan wasan gaba na kungiyar Clermont da tawagar Guinea Mohamed Bayo, mai shekara 23. (Sun)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Dan tawagar Guinea Mohamed Bayo ya dauki hankalin West Ham

Manchester United na duba yiwuwar sayen dan bayan RB Leipzig da Faransa Nordi Mukiele, mai shekara 23. (Fichajes)

Dan gaban Chelsea da Jamus Timo Werner, mai shekara 25, ya so tafiya Manchester United kafin daga karshe ya nufi Stamford Bridge. (Bild)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Kociyan Chelsea ya yaba wa Timo Werner

Tottenham na son sayen dan wasan gaba na gefe na kungiyar Sampdoria da tawagar Denmark Mikkel Damsgaard, mai shekara 21, wanda Juventus ma tana sonsa. (Tuttosport)

Dole ne Arsenal ta biya akalla fam miliyan 38 da rabi idan har tana son sayen dan wasan gaba na Sevilla dan Morocco Youssef En-Nesyri, mai shekara 24. (Mundo Deportivo)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Arsenal na son sayen Youssef En-Nesyri

Manchester City na son sayen matashin dan wasan West Ham da tawagar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 17 Divin Mubama mai shekara 16. (Football Insider)

More from this stream

Recomended