
Asalin hoton, ANADOLU AGENCY
Magoya bayan shugaban na Brazil sun ayyana kotun kolin da majalisar dokoki a matsayin ‘yan kama-karya
Babban alkalin kotun kolin Brazail, Luiz Fux, ya zargi shugaban kasar Jair Bolsonaro da kai hari kan tsarin dimokuradiyya ta hanyar karfafa wa mutane guiwa su yi watsi da hukuncin kotun.
Alkalin ya yi kalaman ne kwana daya bayan da Mista Bolsonaro ya gaya wa magoya bayansa a yayin faretin bikin samun ‘yancin kasar cewa ba zai bi hukuncin alkalan kotun ba.
Asalin hoton, ANADOLU AGENCY
Dubban jama’a sun cika a Paulista Avenue a São Paulo
Mai shari’a Luiz Fux ya yi kalaman ne da ke zaman wata matashi da gargadi ga shugaban kasar da cewa angiza mutane da kalaman kiyayya abu ne da ba za a lamunta da shi ba wanda kuma ya saba wa doka.
Ya ce: ”Tare da cikakken tsari na dimokuradiyya da karsashi na matsayinta Kotun Kolin ba za ta taba yarda da barazana a ‘yancinta ba,, kuma ba za ta mika wuya ga tunzuri ba a yayin da take aiwatar da ayyukanta ba”
Tsawon wata da watanni Shugaba Bolsonaro yake ta kokarin tunzura magoya bayansa ta hanyar nuna bacin ransa a kan wadanda yake kallo a matsayin makiyansa a kotun kolin Brazil.
A yanzu dai yana fuskantar bincike ne daga daya daga cikin alkalan kotun a kan zargin yada labaran bogi.
Yayin da ake gudanar da wannan bincike a kansa shugaban yana kuma barazanar cewa ba zai amince da sakamakon zaben shugaban kasar da za a yi ba a shekara mai zuwa, wanda kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna zai fadi.
Asalin hoton, SOPA IMAGES
Masu hamayya da shugaban su ma sun yi nasu gangamin
Da dadewa Mista Bolsonaro ya yi kokarin sauya tsarin amfani da kwanfuta na zaben kasar, wanda ya ce ana iya tafka magudi da shi, a koma ana amfani da bayar da takardar kada kuri’a.
Daga nan kotun musamman ta zaben kasar ba kawai ta yi watsi da zarginsa ba a matsayin na yada karya, har ma sai da ta bude gudanar da bincike a kan zargin da ya yi cewa za a iya tafka magudi a tsarin
Masu sukansa sun zarge shi da da ɓara irin ta tsohon shugaban Amurka Donald Trump ta zargin magudi idan ya fadi zaben shugaban kasar na shekara mai zuwa.
Yawancin masu nazari na ganin Jair Bolsonaro ba shi da saurin karfi a siyasance ya aiwatar da juyin mulki.
To amma ta hanyar nuna shakku a kan halarcin kotun kolin, ga alama yana shirin kai kasar ta Brazil ga irin rikicin da aka gani ne a ginin majalisar dokokin Amurka, Capitol a ranar shida ga watan Janairu, a lokacin da magoya bayan Shugaba Trump suka mamaye zauren majalisar.
Asalin hoton, ANADOLU AGENCY
Magoya bayan Bolsonaro sun amince da kiransa na a sauya tsarin zaben kasar da ake yi da kwamfuta
Hakan ko ta kasance ne inda shugaban a yayin jawabinsa na bikin samun ‘yanci a babban birnin kasar, Brasilia, inda dubban jama’a suka halarta domin nuna masa goyon baya ya yi kalamai na neman angiza magoya bayan a kan kotun kolin.
Sai dai duk da cewa wasu daga cikin magoya bayan Bolsonaro sun yi nasarar kutsa wa shingen ‘yan sanda a ranar Talata da cikin dare ba su samu damar kewaye ginin kotun kolin ba.
Mista Bolsonaro ya kuma kara caccakar alkalan kotun, inda yake gaya wa gangamin cewa yana matukar farin ciki da dukkanin al’ummar Brazil suka hadu domin sabon ‘yancin kai a kan ‘yan kama-karya na Kwaminisanci a hukumomin shari’a.
Asalin hoton, ANADOLU AGENCY
Dubban jama’a sun cika a Paulista Avenue a São Paulo
A mulkinsa yana yawan samun sabani da alkalan kotun kolin inda har ya yi kokarin ganin an tsige daya daga cikinsu bayan da alkalin ya kaddamar da wasu bincike biyu a kansa.
Da dama daga cikin magoya bayansa sun bukaci da a rufe kotun kolin da majalisar dokoki, suna zarginsu da saba ka’idar aikinsu da kuma gallaza wa Mista Bolsonaro.
(BBCHausa)