Zanga-zangar kin dokokin corona | Labarai

Dubban mutane masu adawa da matakan yaki da corona a tarayyar Jamus, sun gudanar da zanga-zanga a birnin Berlin, duk da matakan da hukumomin kasar suka dauka na haramta zanga-zangar.

Masu aiko da rahotanni sun ce an yi dauki ba dadi tsakanin ‘yan sandan kwantar da tarzoma da masu boren, a yayin da suka kudri anniyar karya shingen ‘yansanda a unguwar “Charlottenburg” da ke yammacin birnin Berlin, kafin yan sandan sun yi amfani da tiyagaz da kulake don tarwatsa masu zanga-zangar, tare da kama wasu da dama.

Fiye da ‘yan sandan kwantar da tarzoma 2000 ne hukumomin Jamus din suka girke a birnin Berlin da zummar murkushe masu zanga-zangar kin jinin matakan yakin da corona da kasar take dauka, suna masu cewa matakan na daga cikin na kan gaba wajen hana ‘yan ci da walwalar jama’a.

More from this stream

Recomended