Manchester United za ta dauki dan wasan Real Madrid da Faransa Raphael Varane a kwangilar shekara hudu a zabin karin shekara daya, sai dai babu tabbas kan ranar da za a duba lafiyar dan wasan mai shekara 28 sakamakon kullen korona. (Athletic – subscription required)
Newcastle na matsa lamba domin ganin ta dauki Axel Tuanzebe, mai shekara 23, daga Manchester United. (Telegraph)
Juventus na son sayar da Aaron Ramsey a bazarar nan a yayin da kungiyar take kallon dan wasan na Wales, mai shekara 30, a matsayin wani jangwam. (Gazzetta dello Sport, via Mail)
Ana sa ran za a duba lafiyar Ben White a Arsenal ranar Laraba a yayin da aka kulla yarjejeniyar £50m kan dan wasan na Ingila, mai shekara 23, bayan sun amince kan cinikinsa da Brighton makon jiya. (Sky Sports)
Romelu Lukaku yana cike da farin ciki a Inter Milan kuma dan wasan na Belgium, mai shekara 28, ba ya shirin barin kungiyar a bazarar nan, duk da zawarcinsa da Chelseatake yi. (Express)
Tottenham ta kara kaimi a yunkurinta na sayen dan wasan Argentina Cristian Romero, mai shekara 23, daga Atalanta a kan £40m. (Telegraph)
Yunkurin Aston Villa na daukar dan wasan Bayer Leverkusen dan kasar Jamaica Leon Bailey ya gamu da cikas sakamakon sha’awar da kungiyoyi irin su Leicester, Everton, Wolves da kuma Southampton suka nuna ta daukar dan wasan mai shekara 23, wanda za a iya sayarwa a kan £30m. (90min)
Juventus ta gaya wa Cristiano Ronaldo cewa tana sa ran zai ci gaba da zama a kungiyar a kakar wasan da muke ciki. Ana rade-radin dan wasan na Portugal, mai shekara 36, zai tafi wata kungiyar a yayin da ya rage sekara daya kwangilarsa ta kare. (Sky Sports)
Har yanzu babu wata kungiyar da ta tuntubi Barcelona domin nuna sha’awar daukar dan wasan Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 30. (Marca – in Spanish)
Xherdan Shaqiri ya shirya tsaf domin barin Liverpool a bazarar nan, yayin da Napoli da Lazio suke cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan na Switzerland, mai shekara 29. (Goal)
(BBC Hausa)