Iran: An jiyo ƙarar mummunar fashewa a arewacin ƙasar

Iran

Asalin hoton, Getty Images

Rahotanni daga arewacin babban birnin Iran na Tehran na cewa an ji wata kara mai karfin gaske, ta fashewar wasu abubuwa da ba a kai ga gano su ba kawo yanzu.

Lamarin ya faru ne a cikin dare a Mellat, wani sanannen wuri da ke kusa da hedkwatar kamfanin watsa labarai birin.

Mataimakin gwamnan Teheran ya ce zuwa yanzu mahukunta na ci gaba da bincike don gano ainihin abun da ya faru.

Kawo yanzu dai babu rahoton mutuwar wani ko jikkatar mutane, sai dai hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda hayaki ya turnuke wajen.

Daga shekarar 2020 ne aka fara samun karuwar hare-haren ban mamaki da suka tarwatsa muhimman wurare a Iran, yawanci wadanda Iran ke amfani da su wajen inganta shirinta na Nukiliya..

An samu tashin gobara da dama da suka lalata kayayyaki a cibiyar nukiliya, matatun mai da cibiyar samar da wutan lantarki, kamfanoni da wuraren kasuwanci a fadin kasar.

Ga wasu daga cikinsu da aka samu a 2020.

  • Ranar 26 na Yuni: An samu fashewa a wurin samar da man da ake amfani da shi a makami mai linzami a Khojir, kusa da Parchin na Tehran; gobara a cibiyar wutan lantarki ta Shiraz, hakan ya haddasa rashin wuta
  • Ranar 30 ga watan Yuni: Wani hari a asibitin Tehran ya yi ajalin mutum 19
  • 2 ga watan Yuli: An samu fashewa da gobara a cibiyar nukiliya ta Natanz
  • Ranar 3 na Yuli: Gobara ta mamaye Shiraz
  • 4 ga watan Yulu: An samu fashewa da gobara a cibiyar samar da wutan lantarki da ke Ahwaz.

(BBC Hausa)

Related Articles