Ronaldo bai yanke kaunar barin Juventus ba, Sancho na sa ran zama dan United

Dan kwallon tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, bai yanke tsammanin barin Juventus kafin kwantiraginsa ya kare a kakar badi ba. Ana alakanta shi da cewat tsohuwar kungiyarsa Manchester United, zai koma. (Express)Dan kwallon tawagar Ingila, Jadon Sancho na sa ran zama dan wasan Manchester United duk da kin sallama tayin fam milyan 67 da Borussia Dortmund ta yi waddake son sayar da matashin mai shekara 21 fam milyan 77 da karin tsarabe tsarabe. (Manchester Evening News)Chelsea ce kan gaba a rige rigen sayen dan kwallon Ingila, Jack Grealish kan fara kakar tamaula, bayan da kungiyoyin Manchester ke zawarcin dan wasan mai shekara 25. (Fichajes via Mirror)Da kyar ne idan sayar da Granit Xhaka‘ daga Arsenal zuwa kungiyar Jose Mourinho Roma zai yiwu saboda kungiyoyin biyu sun kasa cimma yarjejniya. (Corriere dello Sport via Express)

Newcastle United sun kara sunan mai tsaron bayan Liverpool, Nat Phillips cikin wadanda take son dauka a bana, inda za ta yi takara da Burnley don sayen dan wasan mai shekara 24 wanda zai yi zaman benci a Anfiield dazarar Virgil Van Djik da Joe Gomez da kuma Joel Matip sun warke daga jinya. (Mail)Tsohon kocin Celtic Neil Lennon ya ce dan kwallon tawagar Scotland Kieran Tierney, mai shekara 24, zai iya zama dan wasan Manchester (Times – subscription needed)Mai tsaron bayan Real Madrid, Raphael Varane zai bar Sifaniya da taka lede dokin komawa Manchester United ko kuma Paris Saint Germain. Sai dai dan wasan mai shekara 28 yafi son komawa Faransa. Kuma darajarsa ta kao fam miyan 60 ga duk kungiyar da ke son daukarsa. (El Confidencial, via Caught Offside)Mai tsaron bayan Burnley, James Tarkowski na son komawa West Ham a kakarnan. his summer. The 28-year-old England. (Football Insider)Everton ta nuna sha’ar son daukar dan kwallon Sporting Lisbon Matheus Nunes, mai shekara 22. Tun farko ana duba yiwurar salkamar da shi kan fam miliyan 15, da karin tsarabe tsaraben da zai kai fam miliyan biyu kenan zai kai fam miliyan 17 jumulla. (Record, via Daily Star)

More from this stream

Recomended