Kasuwar cinikin ‘yan kwallo: Makomar Dybala, Haaland, Van de Beek, Odegaard

Paulo Dybala

Dan wasan Paris St-Germain dan kasar Argentina Leandro Paredes ya tabbatar cewa shugabannin kungiyar sun shaida masa “kada na yi magana a kan Lionel Messi” a yayin ake rade radin cewa dan wasan na Barcelona mai shekara 33 zai koma Faransa. (Le Journal du Dimanche – in French)

Chelsea na duba yiwuwar sanya dan wasan jamus mai shekara 25 Timo Werner a cikin musayar da take son yi domin dauko dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland, mai shekara 20, zuwa Stamford Bridge a bazara. (Football Insider)

A gefe guda, Manchester United za ta mayar da hankali kan Haaland, yayin da yunkurinta na dauko dan wasan Tottenham mai shekara 27 dan kasar Ingila Harry Kane yake nema ya gagara. (Manchester Evening News)

Dan wasan Netherlands Donny van de Beek, mai shekara 23, yana son barin Manchester United bayan ya kwashe kasa da kakar wasa daya a Old Trafford kuma ya bukaci ganawa da shugabannin kungiyar. (Star)

Arsenal na son dan wasan Real Madrid Martin Odegaard, mai shekara 22, ya ci gaba da zama a Emirates Stadium a kakar wasa mai zuwa, a yayin da kungiyar take neman hanyar sake karbar aron dan kasar ta Norway ko kuma ta saye sh baki daya. (Mail)

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce rahotannin da ke nuna cewa dan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, yana son komawa kungiyar ta Sifaniya a bazara yana iya zama mai kanshin gaskiya. (Sky Italia, via Sky Sports)

Barcelona ta shirya sabunta kwangilar dan wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, wanda a baya ake hasashen zai tafi Manchester United. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Related Articles