
Asalin hoton, Getty Images
Ranar Laraba ne Barcelona ta doke Granada da ci 5-3 a wasan daf da na kusa da na karshe a Copa del Rey na bana.
Kungiyoyin sun tashi wasa minti 2-2 a minti 90 da suka fafata, kuma sai da aka shiga karin lokaci ne Barcelona ta kara sa kaimi ta kai kanta wasan daf da karshe.
Wannan ne karo na 13 da Barcelona ta kai karawar daf da karshe, bayan da a bara a fitar da ita a Quarter finals.
Kaka biyu ce Barcelona ba ta kai daf da karshe ba a Copa del Rey da suka hada da 2009/10 da kuma 2019/20.
Kuma wannan ne karo na 60 da Barcelona ke yin irin wannan kokarin a Copa del Rey wanda it ace kan gaba wajen lashes hi, sai Real Madrid mai kwazo 57 irin kai wa matakin daf da karshe.
Ranar Juma’a za a raba jadawalin daf da karshe a Copa del Rey tsakanin Barcelona da Sevilla da duk wadda ta yi nasara tsakanin Real Betis ko Athletiv Bilbao.
Za a buga karawar daf da karshe gida da waje, inda za a fara wasan farko cikin Fabrairu, sannan ayi karawa ta biyu cikin watan Maris.
Kokarin da Barcelona ta yi kaka 15 a Copa del Rey
- 2020/21 – Daf da karshe kawo yanzu
- 2019/20 -Quarter finals
- 2018/19 – Wasan karshe
- 2017/18 -Lashe kofi
- 2016/17 – Lashe kofin
- 2015/16. -Lashe kofin
- 2014/15 – Lashe kofin
- 2013/14 – Wasan karshe
- 2012/13 – Quarter finals
- 2011/12 – Lashe kofin
- 2010/11 – Wasan karshe
- 2009/10 – Karawar kungiyoyi 16
- 2008/09 – Lashe kofin
- 2007/08 – Daf da karshe
- 2006/07 – Daf da karshe