Champions League: Chelsea da Barcelona da Manchester United sun ci wasanninsu, yayin da Juventus tasha da ƙyar

Da wannan nasara kulob din da Frank Lampard ke horarwa ya kai zagaye na gaba da kwantan wasanni biyu.

Bayanan hoto,
Da wannan nasara kulob din da Frank Lampard ke horarwa ya kai zagaye na gaba da kwantan wasanni biyu.

Chelsea ta kai zagaye na gaba a gasar zakaraun Turai, wasanni biyu kafin a ƙare zagayen farko na gasar.

Hakan ya zo bayan da ta doke kulob din FC Rennes na Faransa da ci 2-1 har gida.

Callum Hudson-Odoi ne ya fara ci wa Chelsea kwallo, kafin masu masaukin baƙin sun farke ta hannun Guirassy.

To sai dai cikin minti na 91 ne Olivier Giroud ya ci wa Chelsea kwallo ta biyu jim kadan bayan shigowarsa.

Da wannan nasara kulob din da Frank Lampard ke horarwa ya kai zagaye na gaba da kwantan wasanni biyu.

A sauran wasannin da a ka buga a daren jiya Talata Manchester ta ɗau fansa kan Istanbul Basaksehir da ci 4-1.

Bruno Fernanadez ne ya ci ƙwallaye biyu tun kafin aje ko’ina, kafin Marcus Rashford da James su ci ƙwallo ta uku da ta hudu.

Itama Barcelona ta shararawa Dynamo Kiev 4-0 har Ukraine, ta hannun Dest da Braithwaite da kuma Griezman.

Bayanan hoto,
Martin Braithwaite

A sauran wasanni PSG ta doke RB Leipzig 1-0, yayin da Lazio ta zubawa Zenith St Petersburg 3-1.

A jamus Borrusia Dortmund ta lallasa Club Brugge 3-0 ta hannun zaƙaƙuran ƴan gabanta Jadon Sancho da Erling Haaland.

A ranar Laraba Manchester City za ta je Girka don karawa da Olympiacos, yayin da Liverpool za ta karɓi baƙuncin Atalanta na Italiya.

Ita ma Real madrid Italiar za ta baƙunta, inda za ta kece reni da Inter Milan.

A sauran wasannin Olympic Maseille za ta kara da Porto, yayin da Bayern Munich masu riƙe da kofi za sauki Red Bull Salsburg a Alliance Arena.

More from this stream

Recomended