‘Yan Najeriya takwas za su shiga gasar Kwallon Amurka ta NBA

NBA Draft

Matasa takwas ‘yan Najeriya aka zaba ranar Laraba da za su buga gasar kwallon kwandon Amurka ta NBA kakar 2020/21.

Ana zabar fitattun matasa 60 da suka kware a kwallon kwando kafin fara wasannin don buga wa kungiyoyin gasar ta Amurka.

Tun farko an tsara zabo ‘yan wasan ranar 25 ga watan Yuni, amma bullar cutar korona ta jawo koma baya, wannan karon ta bidiyo aka yi.

Precious Achiuwa shi ne na uku dan Najeriya da aka haifa a kasar, wanda aka zaba a zangon farko tun 2000, sai Udoka Azubuike na hudu.

Wannan ne karon farko da aka zabi ‘yan Najeriya biyu a zangon farko.

Ranar 22 ga watan Disamba za a fara kakar bana, wadda aka rage yawan wasa 10 zuwa 72, saboda cutar korona.

Haka kuma rage wasannin zai taimaka a kammala gasar cikin sauri, domin ‘yan wasa su samu damar shiga shirin wakiltar kasashensu don tunkarar Olympic a 2021.

More from this stream

Recomended