Ku San Malamanku tare da Sheikh Abduljabbar Kabara | BBC Hausa

Bayanan bidiyo,
Bidyon Ku San Malamanku tare da Shiekh Abduljabbar Nasiru Kabara

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da yake jihar Kano a arewacin Najeriya, kuma shugaban Ƙadiriyya Riyadul Jannah, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya ce babban abin da ya sa a gaba yanzu a rayuwarsa shi ne nazari kan Hadisan Manzon Allah SAW.

Malamin ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da BBC Hausa ke yi a wani shirinta na Ku San Malamanku.

”Babbar hidimar da a yanzu na taƙaita a kanta ita ce Hadisan Maa’aiki Alaihis Salatu Wassalam da bibiyar sawunsu da tantance da bin diddigin sahihan hadisan daga waɗanda suke jabu a cikin hadisin,” in ji shi.

Malamin wanda ya fito daga gidan malanta ya ce buɗar ido ya yi ya gan shi a cikin karatu.

Sheikh Abduljabbar ɗa ne ga marigayi Sheikh Nasiru Kabara, toshon shugaban ɗarikar Ƙadiriyya na Afirka, mahaifiyarsa kuma sunanta Hajiya Hafsah Adussamad.

Shehin malamain ya tashi a Unguwar Kabara da ke cikin ƙwaryar birnin Kano, sannan ya yi makarantar zamani ta Ma’ahad kamar yadda dukkan iyalan Gidan Ƙadiriyya ke yi.

Daga nan ya tafi makarantar Aliya da Makarantar Horar da Malamai ta ATC da ke Gwale, sannan kuma ya je har ƙasar Iraƙi ya yi karatu.

Sai dai malamin ya ce mafi yawan karatuttukan da ya yi duk a gida ya yi su a gaban mahaifinsa, ”a cikin shekara 25 ɗin da na yi tare da mahifina na karatu, fannoni kaɗan ne ban taɓa ba.”

Ƙalubalen da yake fuskanta a gwagwarmayar karatu

Babu wani abu na rayuwa da ke zuwa ba tare da matsaloli ba, musamman a gwagwarmayar karatu da da’awah daga fannin malamai, Sheikh ya ce a nasa ɓangaren abin na da yawa, sai dai kawai wata matsalar ta kan zarce wata.

”Amma wanda ya fi tsaya min a rai shi ne halin da na samu kaina a ciki daga waɗanda su ya kamata a ce na fi samun ɗauki a wajensu wato ƴan uwana ƴan ɗarika, musamman Shehunnai da Malaman Ɗariƙar Tijjaniyya da suka ga kyan mu haɗu mu gina hankar Allah da su, suka kuma kawo min ziyara a cikin wannan waje ta zumunci da ƙauna.

”Na karɓe su hannu bibbiyu kuma muka taru da su muka gina tafiya irin ta da’awah amma a ƙarshe ƙalubalen da na fuskanta daga abin wanda har zuwa yau ban san mene ne sababin da har gobe ya jawo wannan juya baya ba, ta yadda al’amarin ya juye ya zama farmaki.”

Manyan littattafan da ya rubuta

Malam Abduljabbar ya rubuta littattafai da dama amma ya ce babba daga cikinsu shi ne ”Muƙaddamatul azifa” mai shafi 705.

Ya ce littafan nasa na Sunnah sun fi na kowace mazahaba yawa.

Sheikh Abduljabbar na da littafai kimanin 20,000 a ɗakin karatunsa, wanda a mafi yawan lokuta ya kan yi ikirrain cewa zai bayar da su gaba ɗaya idan malamai sun ba shi amsar wata tambaya da ya yi musu, al’amarin da wasu ke ganin tamkar fariya ce.

Sai dai shehin ya ce sam babu fariya a lamarin, ”ƙoƙari ne na jawo hankalin malamai su gane wata masalaha ta gaskiya, musamman irin yadda wasu ke kawo ruɗani da gangan. Idan ba haka ba shi ɗan kallo ba zai fahimci waye yake faɗa masa gaskiya ba.”

Tuwon dawa, yawon duniya

Rai dangin goro in ji masu magana, shi ya sa muka tambayi malam irin abincin da ya fi so, inda ya ce ya fi son tuwon dawa da miyar kuka, amma matarsa ce kawai ta fi sanin irin yadda yake so miyar kukar ta kasance.

A dangin nama kuwa, malam ya ce na rago ne wanda ya fi so.

Dangane da tafiye-tafiye kuwa Malam ya ce a da e ya yi sha’awar wannan amma a yanzu hidimar rubuce-rubucensa ta sa ba ya muradin hakan.

Amma duk da haka ya je ƙasashe da dama musamman a yankin Gabas Ta Tsakiya da suka haɗa da Saudiyya da Iraƙi da UAE da Syria da Iran. Sanna ya leƙa wasu ƙasashen Turai kamar su Rasha.

Ko malam ɗan shi’a ne?

Bayanan hoto,
Wasu da dama na yi wa malamin kallon an shi’a

Wasu da dama na kallon malamin a matsayin mai bin mazahbar Shi’a, sai dai ya ce tuni ya daina musanta cewa shi ba ɗan shi’a ba ne.

Ya ce bai ga dalilin da zai sa a dinga tsorata shi da cewa Shi’a ba aba ce mai kyau ba, inda ya ce a da idan aka tambaye shi yana cewa shi ba ɗan shi’a ba ne, ”amma a yanzu bayan da na yi bincike mai zurfi sai na gane ashe Shi’ar ma ta fi Sunnar hujjoji, sai na ga ba wani dalilin da za a dinga tsorata ni da wannan.”

”Duk wanda ya tambaye ni ko ni ɗan shi’a ne, sai na ce masa mece ce Shi’a a gurinka? Duk amsar da ya ba ni ita ce za ta biyo bayan amsar da zan ba shi.

”Idan ya ce zagin Sahabbai zan ce masa a ina na zage su har ka nasabta ni da shi’a? Sai ka ga babu amsa. Ni dai make-maken nan ne ba zan yi ba don ni ina bayan duk abin da Annabi ya yi umarni ne kawai.

”Kuma a cikin kashi 100 bisa 100 to Shi’a ta fi Sunna gaskiya da kashi 75 a cikin rigingimun da ake da su,” a cewar malamin.

More from this stream

Recomended