Premier League: Arsenal ta ragargaji Fulham a wasan farko

Willian da Aubameyang

Bayanan hoto,
Willian ne ya bayar aka ci duka ƙwallo uku a wasan na yau

Baƙin fuska a tawagar Arsenal Gabriel da Willian sun taka rawar gani yayin da ta casa Fulham har gida a wasan farko na kakar Premier ta 2020-21.

Da hannun tsohon ɗan wasan na Chelsea a duka ƙwallo uku da Arsenal ta zira a ragar masu masaukin baƙin.

Shi ma Gabriel wanda aka cefano kan fan miliyan 23 daga Lille, ya ci ɗaya a wasansa na farkon.

Arsenal ta murza leda yadda ya kamata, yayin da ‘yan bayan Fulham suka riƙa haifar wa kansu da matsaloli.

Alexandre Lacazette ne ya fara jefa ƙwallo a minti na 8 kafin Gabriel ya ƙara ta biyu minti huɗu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Ana minti na 57 ne kuma Aubameyang ya ci ƙwallo mai matuƙar kyau bayan ya buɗa ɓangren hagu kuma ita ce ƙwallo ta 86 da ya ci wa Arsenal a Premier cikin kakar wasa huɗu.

(BBC Hausa)

More from this stream

Recomended