Gwamnatin Buhari bulunbituwa ta ke yi – Masana

Bayanan sauti
Rahoton Ibrahim Isa

Ƙudurin gwamnatin Najeriya ƙarƙashin Shugaba Muhammadu Buhari na faɗaɗa manufofinta guda uku – inganta tsaro da bunkasa tattalin arziki da kuma yaki da rashawa zuwa wasu muradai guda tara ya tayar da ƙura.

Wasu jama’ar ƙasar na ganin da sake ganin cewa alƙawuran da ya ɗauka tun farkon mulkinsa bai cika su ba yayin da wasu kuma ke ganin Shugaban ya yi abin yabawa musamman yadda gwamnatin ta iya kawo sauƙin matsalar tsaro.

Dr Usman Bugaje masanin harkokin ci gaban ƙasa ya ce akwai shawarwari da dama da aka bai wa Shugaba Buhari lokuta daban-daban amma shiru.

“Idan da gaske yake yana so ya yi wani abu, akwai abubuwa uku da zai yi ya nuna mana da gaske yake, waɗannan shugabannin ɓangaren sojoji duk ya canja su, don sun kasa lokacinsu ya wuce, na biyu ya kama ɓarayin da ke kusa da shi kafin ya kama na nesa.” In ji Dr Bugaje

Sai dai wani masanin tattalin arziki a kwalejin fasaha ta Kano Mallam Habib Lawan ya ce akwai buƙatar gwamnati ta ginu a kan wasu ginshikai kafin ta cim ma muradan nata.

Ya ƙara da cewa ya kamata a tabbatar da gwamnati ta jama’a domin jama’a don a yi wa jama’a a aiki.

Amma mai bai wa shugaban shawara kan kafafen yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya ce gwamnatin shugaba Buhari ba ta gaza ba, “farashin abinci ya tashi amma gadarar shugaba Muhammadu Buhari shi ne yanzu ai bama shigo da abincin da muke ci daga ƙasar waje.

Maganar rashawa da cin hanci, yanzu idan mutum ya yi yasan akwai mataki da zai biyo baya.” a cewar Garba Shehu.

A baya ma babbar jam`iyyar hamayya ta PDP ta ce gwamnatin APC mai muki ta rasa abin fada ne, kawai, ta tsaya tana dawuwari a waje guda, alhali lokaci ya kure mata kamar yadda Mista Kola Olagbondiyan sakataren yada labaran jam`iyyar ya faɗa.

More from this stream

Recomended