Manchester United ta yi sakacin kasa hawan mataki na uku a teburin gasar Premier League, bayan da ta tashi 2-2 da Southampton ranar Litinin a Old Trafford.
Stuart Armstrong ne ya fara zura kwallo a ragar Manchester United a minti na 12 da fara tamaula.
Hakan ne ya sa United ta tuna cewar Southampton ce ta ci Manchester City 1-0 ranar 5 ga watan Yuli a gasar Premier League.
Dalilin da ya sa kungiyar da ke karbar bakuncin karawar a Old Trafford ta kara kwazo ta farke a minti na 20 ta hannun Marcus Rashford.
Kuma tun farko sai da Rashford ya zura kwallo a ragar Southampton, amma mataimakiyar alkalin wasa ta ce ya yi satar gida.
Minti na uku tsakani da United ta farke ne, Anthony Martial ya ci mata na biyu, kuma kowa ya bai wa kungiyar ta koma ta uku a kan teburi kenan.
Wasan ya yi zafi matuka an yi kazar-kazar tsakanin kungiyoyin biyu, kuma tun kan hutu aka zura kwallaye uku a raga.
Bayan da suka sha ruwa suka huta aka koma zagaye na biyu ne wasa ya canja fasali, inda Southampton ce ta rike kwallo kaso 52 cikin 100.
Haka dai kungiyar ta ci gaba da sa kaimi har sai da farke a karin lokaci wato minti na 96 ta hannun Michael Obafemi.
Da wannan sakamkon United tana nan ta biyar da maki 59, iri daya da na Leicester City ta hudu da tazarar maki daya tsakaninta da Chelsea ta uku a teburin bana.
Ita kuwa Southampton tana ta 12 a teburi da maki 45, kuma sakamakon nan ya yi mata kyau, ita ma tana harin gurbin Europa League na badi.
Wannan sakamakon da kungiyar ta Old Trafford ta tashi da Southampton ya sa ta yi wasa 18 a jere ba a doke ta ba kawo yanzu.
Rabon da a yi nasara a kan United tun ranar 22 ga watan Janairu a karawar Premier League da Burnley ta ci 2-0 a Old Trafford.
Cikin wasa 18 da ba a doke ta ba ta ci karawa 12 da canjaras shida ta kuma ci kwallo 48 aka zura mata takwas a raga.
Bayan buga wasan mako na 35, United za ta je gidan Crystal Palace ranar 16 ga watan Yuli a ci gaba da karawar mako na 36 a gasar ta Premier League.
A kuma ranar Southampton za ta karbi bakuncin Brighton a St Mary.