Amurka ta sanya wa ‘yan Najeriya takunkumi saboda damfara

Donald Trump

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Amurka ta ce ‘yan damfarar sun yi sojan gona a matsayin shugabannin kamfanoni

Hukumomin Amurka sun sanya takunkumi wa wasu ‘yan Najeriya shida da ake zargi da aikata zamba da ta kai ta dala fiye da miliyan shida ta intanet.

A cewar wata sanarwa ta Sakataren harkokoin wajen Amurka Mike Pompeo, wadanda ake zargi da damfarar karkashin jagorancin wani mai suna Richard Uzuh, sun yi sojan gona a matsayin shugabannin kamfanoni inda aka tura masu miliyoyin daloli ba bisa ka’ida ba ta asusun banki.

Sauran mutanen su ne Michael Olorunyomi, Alex Ogunshakin, Felix Okpoh, Nnamdi Benson da Abiola Kayode.

Sun kuma yaudari wadanda suka fada tarkonsu, domin samun lambobin sirri, da lakabi, da makullan asusu, da sauran bayanansu na banki.

‘Yan damfarar sun raba dala fiye da miliyan shida a cikin tsarin na zamba.

Wadanda suka fada tarkon soyayyar boge na ‘yan damfarar da ake zargi kuwa, an yaudare su ne ta hanyar sakwannin imel da kuma ta shafukan sadarwar intanit.

Sanarwar ta ce ‘yan Najeriyar sun tsere kuma ana ci gaba da nemansu ruwa-a-jallo.

Sai dai kuma hukumomin Amurka sun ce an karbe ikon dukkan kadarorinsu, da wasu abubuwan bukatunsu da ke cikin Amurka ko wadanda ke gittawa ta cikin Amurka, kuma an haramta wa Amurkawa hulda da su kowacce iri.

Mike Pompeo ya ce masu mugun nufi na amfani da ci gaban fasahar zamani domin cutar da Amurkawa masu rauni, amma hukumomi sun tashi haikan domin dakile mazambatan.

Gagarumin shiri

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumomin Amurka sun ce ‘yan Najeriyar sun yi hakon daidaikun Amurkawa ne da kuma kananan harkokin kasuwanci a sassa daban-daban na kasar ta Amurka a wani abu da Sakataren Harkokin Waje Mike Pompeo ya kira ”gagarumin shiri” na cutarwa ta hanyar imel da kuma soyayya ta boge.

Hukumomin Amurka sun ce wadanda matsalar ta rutsa da su sun hada da manya da yara, da masu zurfin ilmi da marasa shi, da kuma wadanda suke matakai daban-daban na karfin arziki a sassa daban-daban na Amurka.

Amma galibin wadanda aka damfarar mata ne da da dattawa da kuma wadanda suka rabu da miji ko matar aurensu.

Gwamnatin Amurka dai na nuna matukar damuwa kan matsalar zamba ta intanit, inda a watan Yulin bara, Sashen Dakile Laifuka na Ma’aikatar Kudin Amurka ya bayyana cewa ya samu korafe-korafe fiye da 32,000 da suka shafi yunkurin damfarar cibiyoyin kudi na Amurka da abokan huldarsu kimanin dala biliyan tara.

A watan Agustan shekarar da ta gabata dai hukumomin Amurka sun ce an tuhumi ‘yan kasashen waje kimanin 80 bisa zargin laifukan zamba ta intanit, da suka shafi yunkurin damfara ta kimanin dala muliyan 46, galibinsu ‘yan Najeriya.

A lokacin mutum 14 kacal suka sanar da kamawa, sauran kuma suna zaune a kasashen waje, kuma hukumomin Najeriya a lokacin sun yi wa Amurka alkawarin hadin kai domin kama wadanda ake zargi da ke zaune a Najeriya.

Babu tabbaci ko mutane shida na baya-bayan da Amurka ta dirar wa na cikin mutanen da aka tuhuma a bara.

Related Articles