Kusan shekaru 4 kenan da gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin ba da tallafi ga marasa karfi da nufin yaki da talauci a kasar. Sai dai an yi ta samun koke-koke tun bayan kaddamar da shirin cewa ba ya kaiwa ga wadanda aka yi domin su.
Annobar coronavirus ta sake dagula al’amura da dama a kasar, inda ake samun sabanin fahimta tsakanin masu kula da gudanar da shirin da kuma majalisar wakilai ta kasar da ke kokarin kafa doka don akai ga cimma manufar samar da shirin.
Tun bayan ayyana tallafi ga ‘yan Najeriya marasa karfi da gwamnatin kasar ta yi saboda bullar cutar coronavirus, aka fara samun sabani tsakanin ma’aikatar ayyukan jinkai dake kula da shirin da majalisar dokokin kasar a kan yanayin zakulo mabukata da ke cin gajiyar shirin, da mika bukatar karin bayanin a kan kundin bayanan wadanda suka ci gajiyar shirin.
A ranar juma’a da ta gabata majalisar wakilai ta bakin shugabanta, Femi Gbajabiamila ta bayyana cewa, za ta samar da doka da za ta taimaka wajen kula da shirin, tare da daidaita lamuran ba da tallafin inganta rayuwa na “Social Investment”.
Femi Gbajabiamila, ya ce dokar za ta tsara yadda za’a sami mabukata a ba su tallafi, da ya hada da ciyar da yaran makaranta, tallafin matasa na N-power, Trader Moni da dai sauransu, kamar yadda ya kamata ba wai a hannun wasu tsiraru ba.
Ministar ayyukan jinkai ta Najeriya, Sadiya Umar Faruk, ta yi karin bayani a kan yadda aka fara aiwatar da shirin ciyar da yaran makaranta a gida ta hanyar yin amfani da kundin bayanan makarantun su.
Wasu ‘yan Najeriya sun koka game da yadda tallafin gwamnati bai isa gare su ba, inda farfesa Sani Abdullahi, mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum ya ce, majalisar wakilai na da hurumin samar da wannan dokar.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Halima Abdulrauf.
[ad_2]