
Hakkin mallakar hoto
BBC/NHU
Wani marayan biri a maƙale kan bishiya da mai kula da shi
Yayin da duniya ke fama da dokar kulle, wasu matasa a wani aji na daban na ci gaba da daukar darasi.
A wata makaranta a cikin dajin, wani dan karamin biri na koyon yadda ake hawa bishiya daga wajen uwar rikonsa.
Marayun na kwashe sa’o’i 12 a ko wacce rana a cikin daji, don shirya wa sabuwar rayuwa a cikin daji.
Ana daukar rayuwar birran tare da hotunansu kafin cutar korona ta dakatar da komai, ana haska wa a wani shirin BBC One.
Da samun alakar da suke da mutane a kullum, rayuwar na kara kyau a wajen dabbobin, in ji Dakta Signe Preuschoft, shugabar wani shirin tallafawa birrai, wadda kuma ke lura da wata cibiyar gyaran halayyar da ke gabashin Kalimantan.
A matsayin matakan kariya, ma’aikata na da na’urar duba zakin jiki, kuma suna sa takunkumi.
- An tsinci wata yarinya da ke rayuwa da birrai a daji
- ‘Na sayar da gashina dala biyu don na saya wa ‘ya’yana abinci’
Wannan annoba ta kawo tsaiko ga shirye-shiryen tattaunawa masu yawa a duniya, amma Dakta Preuschoft ta ce hakan ya bijiro da wasu sabbin sauye-sauye masu kyau da ta kawo.
“Akwai damar kare rayuwar dabbobi sama da yadda ake yi a baya wanda ba su halarta da kuma kasuwancinsu da kuma cin namansu. “Abu ne da ke buƙatar ilimi.”
Hakkin mallakar hoto
Jejak Pulang/FOUR PAWS
Dakta Preuschoft tare da wata marainiyar biranya
Iyayen rikon na taimakawa wadannan matasan birran wajen iya hawa bishiya, wanda wannan kwarewa ce da ya kamata su samu wajen iyayensu na haihuwa.
Za su kasance suna kwashe lokaci mai yawa a kan doron kasa, maimakon inda halittu irin su suka fi zama su ci abinci su yi barci su kuma rayu a saman bishiya.
Kananan birran na da wata dama yayin hawa bishiya, saboda za su iya maƙale dan karamin reshe cikin sauƙi, in ji Dakta Preuschoft.
“Za ka ga yawancin marayun birran na jin dadi matuka lokacin da suka gansu a sama tare da iyayensu mata na riko,” a cewarta.
Ana janye wannan dokar hana fitar, za su koma ainihin wajen zamansu cikin daji. An koya musu duk wani abu da ya dace na kwarewa ta yadda za su iya kare kansu a cikin dajin da ke tsakanin biranen Balikpapan da Samarinda.
Hakkin mallakar hoto
BBC/NHU
Dakta Signe Preuschoft tare da tawagarta da ke sha’awar aikin gyaran halayya a dayke da jariran birrai
Munufar ita ce ba su kariya daga masu fasa kaurin dabbobin, da kuma tarbiyantar da mayu daga cikinsu, da manufar sakinsu su koma cikin daji su ci gaba da rayuwarsu.
Nau’in wadannan birran na Bornean ba su fi 50,000 ba ne kawai suka rage a duniya, yayin da adadin hallitarsu ke raguwa cikin shekara 70. Karancin samun ruwan sama zuwa gonaki kwakwar manja zuwa hakar kwal wanda ya haifar da rikici tsakanin ‘yan adam da birran.
Ana kwace wadannan marayun birran ne daga hannun matattun iyayensu mata, a sayar da su ko kuma fasa kaurinsu.