![Women protest outside the Saudi consulate in New York on 1 June 2019 to protest against the trials of three clerics in Saudi Arabia](https://arewa.ng/storage/2020/04/Saudiyya-za-ta-daina-aiwatar-da-hukuncin-kisa-kan-kananan-yara.jpg)
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Amnesty ta ce Saudiyya ta yanke hukuncin kisa kan mutum 184 a 2019
Saudiyya ta sanar da cewa daga yanzu ta daina yanke hukuncin kisa kan wadanda suka aikata laifuka yayin suna yara kanana.
Hukumar da ke kula da hakkin dan Adam ta kasar ce ta bayyana haka.
Sarki Salman ya sanya hannu kan dokar tabbatar da sanarwar wadda ta zo kwana biyu bayan da Sarkin ya hana yi wa masu laifi bulala a kasar.
Hukumar kula da hakkin yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya – wadda kasar Saudiyya mamba ce ta hukumar ta ce irin wannan hukunci bai kamata a rika yanke shi kan kananan yara ba.
Masu fafutukar kare hakkin bil Adama na cewa Saudiyya na cikin jerin kasashe masu gallaza wa al’ummarsu a duniya.
Sun ce ana matukar hana mutane fadan albarkacin bakinsu musamman a fagen sukar gwamnati, domin anan iya kama su babu shari’a.
Saudiyya ta yanke hukuncin kisa kan mutum 184 a 2019, inji Amnesty International. A cikinsu akwai wani mutum da aka yanke wa hukuncin kisa kan laifin da ya aikata a lokacin yana yaro.
Hukumomin Sauddiyya ba su sanar da ranar da dokar za ta fara aiki ba.