
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Maurizio Sarri da ‘yan wasan Juventus sun yafe albashin wata hudu domin ceto kungiyar daga tabarbarewar tattalin arziki sakamakon coronavirus.
Kudin da Juventus za ta samu zai kai fam miliyan 90, kwatankwacin Dallar Amurka miliyan 80 a wata hudun da ba ta biya albashinba.
An dakatar da dukkan wasanni a Italiya zuwa 3 ga watan Afirilu, don gudun yada cutar.
Fitattun ‘yan wasan Juventus da suka hada da Cristiano Ronaldo da Aaron Ramsey da dai sauransu, ba za su karbi albashin watan Maris da Afirilu da Mayu da kuma na Yuni ba.
Kafin a tsayar da gasar Serie A ta Italiya, Juventus ce ke kan gaba a teburi da tazarar maki daya tsakaninta da Lazio.
Juventus ta gode wa masu horas da tamaula da ‘yan wasa kan wannan kokarin da suka yi a lokacin da ake mawuyacin hali.