
Hakkin mallakar hoto
Twitter/@jidesanwoolu
Jihar Legas da ke kudancin Najeriya inda cutar numfashi ta coronavirus ta fi kamari a kasar ta sanar da matakinta na samar da wata cibiyar killace masu fama da cutar.
Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ne ya sanar da haka a shafin Twitter inda ya ce gwamnatinsa ta yi hadin gwiwa ne da bankin GT, daya daga cikin bankunan da ke gudanar da harkokinsa a kasar wajen samar da cibiyar.
A cewarsa, cibiyar na da karfin daukar marasa lafiya 110 musamman wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ta covid-19.
A jihar ta Legas, mutum 59 ne suka kamu da coronavirus cikin mutum 97 da ke dauke da cutar a Najeriya.
Gwamnan ya sake jaddada kudirinsa na ganin an yaki coronavirus a jihar tare da rage bazuwarta musamman daga mutanen da suka dawo daga kasashe waje.
Kazalika, Ma’aikatar Lafiya a Legas din ta yi hasashen cewa mutum 39,000 ka iya kamuwa da cutar a jihar.
Sai dai gwamnatin jihar na ci gaba da daukar matakai daban-daban na hana bazuwar cutar ciki har da umartar mutane su zauna a gida tare da nesa-nesa da juna.
Gwamnatin ta kuma daukin matakin yin feshin magani domin kashe kwayar cutar ta covid-19.
Hakkin mallakar hoto
Twitter/@jidesanwoolu
Sabuwar cibiyar kebe masu fama da coronavirus a Legas
Haka ma hukumar dakile yaduwar cutuka a Najeriya NCDC ta ce mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka Aliko Dangote ya ba ta gudummawar motocin daukar marasa lafiya har hudu domin tallafa musu a kokarin da ake na dakile bazuwar cutar a Najeriya musamman a jihar Legas.
Hakkin mallakar hoto
Twitter/NCDC
Motocin da attajirin Afirka Aliko Dangote ya bai wa gwamnatin Legas domin yaki da coronavirus
Baya ga Dangote, akwai wasu attajira a Najeriya da suka ba da gudummawar kudi domin dakile cutar a kasar.