
A karon farko fiye da mutum 100 sun mutu sakamakon coronavirus a Birtaniya a kwana daya.
Adadin mutanen da suka mutu ya tashi daga 475 zuwa 578, a cewar jami’an kiwon lafiyar kasar.
An yi wa mutum 104,866 gwajin cutar, kuma a cikinsu mutum 93,208 ba sa dauke da ita yayin da mutum 11,568 suke da coronavirus