Wakar da Sulaiman Ibrahim na BBC ya yi wa Mata | BBC Hausa

Mintuna 6 da suka wuce

Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron wakar.

Wakar da Sulaiman Ibrahim na BBC ya yi wa Mata albarkacin Ranar Mata Ta Duniya.

Mun taba wallafa wannan wakar a ranar 8 ga watan Maris din 2018, kuma mun kara wallafa ta ne a 2020 domin kara murnar zagayowar wannan rana.

A cikin wakar ya wake iyaye mata inda har ya ce lallai da bazarsu ake rawa.

Ga dai yadda wakar take a rubuce:

Mata da bazarku muke rawa,

Ko ga kyauta zumuncin ‘yan’uwa,

Hairin da kuke bai sokuwa,

Kyautuwarmu mu yi maku godiya.

Ku ma da bazarmu ku wataya,

Lambu da baza mashahuriya.

Haka, sonmu ga ku ba tantama,

Don cinku da shanku mu fantsama,

Rayuwarmu ku san mun cinjima,

Rijiyar kaunarku a zuciya.

Yau a kan hairinku nake tafe,

Wanda ke bobboye a rurrufe,

In fitar sarari in kakkafe,

Babba, yaro, mai rarrafe,

Kowa ya gani ya yi godiya.

Na san wasu sun fi guda dari,

Ko da wasu kun yi a zahiri,

Kadan ne sun ka yi tambari,

Na fahimta ko ba tambaya.

Kun dauki cikinmu wata tara,

Wani ko ya dade nufi shekara,

Kwarnafi da amai da su gantsara,

Dukkan su a kanku su tattara,

Su hana ku zama ko kwanciya.

Nakuda ta taho sai zullumi,

Wahalar wasu ta isa tagumi,

Wasu dai su haye ba ko gumi,

Wasu ko rayuwa suka sallami,

Haihuwa ta raba su da duniya.

Tun muna ‘yan yara kankana,

Tumbudi da fitsari ko’ina,

Sai ku wanke babu kuna tsana,

Wanka da ado duka ku yi mana,

Na shiga tsara a yi fariya.

Matan aure na cikin gida,

Kun tsare in har ba mai gida,

Martaba da mutunci har bida,

In ba ku ya kwashe dukiya.

Duk gida bai rayo sai da ku,

Mai gida shi kan shi ya kan zaku,

Ya taho ga gida, in dai da ku,

Ba don ba tuwo ko kudaku,

Ko don fara’arku da dariya.

Koko su furar sha sun daka,

Dadi nata na kai har a ka,

Ka ga sai noma ba kwanciya.

Ko a daji ko a cikin gari,

Kankana na bisa da takarkari,

Sai da su aka kai nono gari,

Har kashi har naman yin miya.

Wasu kasunni aka ci da su,

Su zane, riga, nan ma da su,

A sayen haja kuma ba ya su,

Sannan kuma kansu akwai rufa,

Aikin da suke sun dukufa,

Malamar jinya ke ma kuwa,

Tanyon da kike ya na dan’uwa,

Gun mai kyanda ko motsuwa,

‘Yan zuwa kullum ko kwanciya.

Wasu malanta suka sa gaba,

Gun karantarwa ba a bar su ba,

Natsuwar ilmi ba a fi su ba,

Mai jahilci ya yi tambaya.

Wasu matan su sun cin mana,

Ilmi wasu ma sun dar mana,

‘Yan taru su ta ka tattara,

Har su san ilmi kuma su yi zara,

Don su zan su ma sun zabura,

Ga sanar da matan karkara,

Ilmin addin da na duniya.

Yau ko wasu matan sun sake,

A fagen ilmi sun shantake,

Matan wasu sassan yau suke,

Kallon su kamar shanun sake,

Tun da dai da bazarku muke rawa,

Ya kyautu ku san dokin hawa,

Ga bida ta sani ku yi sukuwa,

Don da shi aka waye kai kuwa,

Har a sami abin yin tutiya.

Ko can mata ba a bar su ba,

Yau ma wasu matan na gaba,

Don fa mata in ba hada ku ba,

Ba a iske kasa na ci gaba,

To nan mata zan ce da ku,

Sulaiman Ibrahim ke maku,

Fata hairi ya ishe ga ku,

Sallama ta kwarai ta tarar da ku,

Ko’ina kuke wannan duniya.

More from this stream

Recomended