Shugaban hukumar EFCC, Malam Ibrahim Magu, ya ce hukumar na bukatar a hada hannu da al’umma don cimma nasarar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
Shugaban hukumar ya kara da cewa, tsarin kotu na matukar kawo cikas ga hukumar EFCC wajen kwato dukiyar da ake zargin an sace.
Malam Ibrahim Magu ya kuma warware damuwar da wasu yan-kasa ke nunawa ta yadda za a yi amfani da kudin da hukumar EFCC ke karbowa.