Jirgin yakin Saudiyya ya yi hatsari a Yemen | BBC Hausa

'Yan tawayen Houthi na Yemen

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Saudiyya na yaki da ‘yan tawayen Houthi a kaar Yemen tun a shekarar 2015

Wani jirgin yaki mallakar Saudiyya na rundunar hadin gwiwar da kasar ke jagoranta a yakin Yemen ya fado a yankin al-jawf na arewacin Yemen din.

Mai magana da yawun rundunar ya tabbatar da cewa jirgin Saudi Tornado “ya fado” yayin da yake kai agaji a kusa da sansanin rundunar sojin Yemen, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA.

‘Yan tawayen Houthi a Yemen sun ce su ne suka harbo jirgin.

Rundunar karkashin jagorancin Saudiyya, tana na yakar ‘yan kungiyar Houthi tun a shekarar 2015.

Ta shiga kasar ne bayan kungiyar ta tumbuke gwamnatin da kasashen duniya ke mara wa baya daga mulki a babban birnin kasar Sanaa.

‘Yan Houthi sun ce sun yi amfani da makamin roka daga kasa zuwa sama domin harbo jirgin a ranar Juma’a.

Sun zargi rundunar ne da kashe mutum 30 a wani harin ramuwar gayya a al-jawf ranar Asabar.

More from this stream

Recomended