A daidai lokacin da ake kara samun yawaitar kai hare-hare a Najeriya, ministan sadarwa a kasar, Dakta Isa Ali Pantami, ya yi ikirarin cewa ‘yan ta’adda na amfani da shafukan sada zumunta na zamani domin daukar sabbin mambobi da kuma tsara yadda za su kai hare-hare.
Ministan ya bayyana cewa akwai bukatar samar da hanyoyin hikima wajen dakile ta’addanci da kuma hana faruwarsa baki daya.
A tattaunawar da BBC ta yi da Mohammed Hamisu Sharifai, wani mai karatun digiri na uku kan tsaro a shafukan intanet, ya tabbatar wa BBC da cewa lallai kungiyoyi masu kai hare-hare a Najeriya da wasu kasashen ketare na amfani da shafukan intanet domin daukar mambobi da kuma yin magana a tsakaninsu a sirrance.
Hamisu Sharifai yayi mana karin bayani dangane da wani shafi na ‘Dark Web’ wanda ya ce shafi ne da ake amfani da shi wajen aikata ayyukan masha’a.
Ya ce ana amfani da shafin wajen cinikin kwayoyi da hayar masu kisan mutane da kuma aikata duk wasu mugayen abubuwa da dan adam zai iya tunani.
Sai dai ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na da kalubale gabanta dangane da kara inganta tsaro a shafukan sada zumunta.
Ya ce ”samar da tsaro ba karfin soja bane kawai, ya kamata kasar ta waiwayi bangaren samar da bayanan sirri na zamani”.
Ya ce akwai fasaha daban-daban kuma akwai ‘yan kasar da ke da kwarewa kan wannan bangaren inda ya ce ya kamata gwamnati ta mayar da hankali ta fannin domin samun nasara.