Ndume ya roki Buhari ya kawo karshen rikicin Boko Haram | Arewa News

Harin Auno

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ndume ya ce akwai sakaci a harin Auno inda aka kashe mutum 30

Shugaban kwamitin sojan kasa a Majalisar dattijai a Najeriya, Sanata Ali Ndume ya nanata bukatar a gudanar da bincike kan harin da aka kai Auno wanda ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum 30.

Ya ce bala’in da rikicin Boko Haram ya jefa al’ummar arewa maso gabashin kasar musamman ma jihar Borno, ya isa haka nan inda ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakin kawo karshensa.

Harin na Auno wanda aka kai a daren Lahadi na daga cikin hare-haren ‘yan ta-da-kayar-baya mafi muni a baya-bayan nan.

Mayakan sun kai harin ne da yayin da matafiyan ke barci cikin motocinsu bayan jami’an tsaro sun hana shiga birnin Maiduguri daga misalin karfe biyar na yammaci.

  • Yadda Boko Haram suka kona mutane da ransu a Auno
  • Yadda gwamna ke kallon rikicin Boko Haram a Yobe

Tun da farko tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Kashim Shettima ne ya fara kiran a gudanar da bincikekan harin.

A nasa bangaren kuma Sanata Ali Ndume da ke wakiltar Borno ta kudu ya ce “akwai sakaci, don haka nake goyon bayan kiran da Kashim Shetima ya yi cewa ya kamata a gudanar da bincike.

Sanatan ya kuma roki gwamnati ta taimaka wa wadanda suka yi hasara harin da aka kai a Auno.

“Girman barnar da aka yi a Auno ya wuce misali, mutum sai ya je ya gani da idonsa,” in ji Ndume.

Sanatan ya kuma yi kira ga shugaban kasa da jami’an tsaro su tausayawa mutanen Borno a kawo karshen rikicin da ya ce ya addabi Borno tsawon shekaru 10.

“Don Allah muna rokon gwamnati ta taimaka ta kawo karshen wannan matsalar ko da kuwa sojojin haya za ta dauko ta shigo da su Borno, idan zai taimaka a kawo karshen rikicin.”

“Muna nan muna binne mutanenmu ana muna barna kuma gwamnati tana da dama za ta iya magance wannan matsalar da ta addabe mu shekaru 10,” in ji shi.

Related Articles