
Hakkin mallakar hoto
PA Media
Ed Woodward
An kai hari gidan babban mataimakin shugaban kulob din Manchester United Ed Woodward.
Wani gungun jama’a ne suka kai harin suna rera cewa ‘za ka mutu.’
To sai dai ba su yi nasarar samun Woodward a gida ba a lokacin.
Wani hoton bidiyo da aka saka a sashen sada zumunta ya nuna wasu mutane na jefa jar tuta a cikin gidan Mista Woodward.
A martani kan harin, kungiyar Manchester United ta ja kunne cewa duk wanda ta kama da laifin kai harin za ta hana shi shiga kallon wasanni har abada.
Sanarwar da kungiyar ta fitar na cewa ‘Magoya baya na da damar bayyana ra’ayinsu kan abinda ke faruwa, sai dai nuna fushi ta hanyar saka rayuwar wani mutun cikin hadari ba abu ne da za mu lamunta ba.”
Kungiyar ta sanar da cewa za ta cigaba da aiki da hukumar ‘yan sanda don gano maharan.
Woodward ya dade yana fuskantar matsin lamba inda magoya bayan kungiyar ke masa kallon ummul haba’isin matsalolin da kulob din ya shiga.
Manchester United na zaune ne ta biyar a teburin Gasar Firimiya da maki 33 tsakaninta da Liverpool mai jan ragamar teburin, kuma da yawa daga cikin magoya bayan kungiyar na ganin laifin Woodward ne.
Ko a wasannin da kungiyar ta buga na baya-bayan nan da Burnley da Tranmere, magoya bayan sun yi ta rera wakokin kin jinin Mista Woodward da kuma iyalan Glazer da ke da kungiyar.
Wannan ba shi ne karon farko da ake harar masu kungiyar ba.
Ko a shekarar 2004 an taba kai wa motar daraktan wasanni a kungiyar Maurice Watkins hari, wanda daga karshe ya sayar da kasonsa ga Malcolm Glazer.
United za ta fuskanci abokiyar hamayyarta Manchester City mai makwabtaka a wasan kusa da na karshe zagaye na biyu na kofin Carabao da City din ke rike da shi.
A zagayen farko Manchester United ta yi rashin nasara da 3-1 har gida.
Aston Villa ta doke Leicester da ci 2-1
A dayan wasan kusa da na karshe da aka buga ranar Talata, Aston Villa ta doke Leicester da ci 2-1, ta na kuma jiran buga wasan karshe tsakanin a tsakanin United da City.