Sunshine da Pillars sun raba maki tsakaninsu | BBC Hausa Sport

Week 17

Hakkin mallakar hoto
NPFL

Sunshine Stars da Kano Pillars sun tashi 2-2 a wasan mako na 17 a gasar Firimiyar Najeriya da suka kara ranar Lahadi.

Anthony Omaka ne ya ci wa Sunshine kwallaye biyun, shi ma Auwalu Ali ne ya ci wa Pillars kwallayenta biyun.

Da wannan sakamakon Pillars ta hada maki 21, ita kuwa Sunshine tana da 27 kenan.

Pillars za ta karbi bakuncin Adamawa United a wasannin mako na 18, ita kuwa Sunshine Stars za ta ziyarci Heartland domin fafatawa a filin wasa na Okigwe Township stadium.

Sakamakon wasannin mako na 17:

  • Abia Warriors 1-0 Wolves
  • Katsina Utd 1-0 FC Ifeanyiubah
  • Akwa Utd 3-1 Heartland
  • Sunshine Stars 2-2 Kano Pillars
  • Adamawa Utd 2-1 Kwara Utd
  • MFM 0-0 Plateau Utd
  • Rivers Utd 0-0 Wikki
  • Lobi 2-1 Nasarawa Utd

Tun a ranar Asabar aka kara a wasa daya

Dakkada 2-0 Jigawa GS

More from this stream

Recomended