Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon nan, daga BBC Hausa

Makada da mawaka sun cashe a wajen bikin bude gasar kwallon kurket ta 'yan kasa da shekara 19 ta duniya ranar Juma'a gabanin fafatawar da aka tsakanin mai masaukin baki, Afirka ta Kudu da Afghanistan a Kimberley.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Makada da mawaka sun cashe a wajen bikin bude gasar kwallon kurket ta ‘yan kasa da shekara 19 ta duniya ranar Juma’a gabanin fafatawar da aka yi tsakanin mai masaukin baki, Afirka ta Kudu da Afghanistan a Kimberley.

A rana ce kuma wadannan mutanen 'yan kabilar Samburu a Kenya suka yi rawa yayin da ake yi ruwa farin dango.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

A ranar ce kuma wadannan mutanen ‘yan kabilar Samburu a Kenya suka yi rawa yayin da ake yi ruwa farin dango.

A can Nairobi, babban birnin Kenya, masu fafutika ne suka yi gangami domin tunawa da ranar Yaki da Talauci ta Duniya. Suna neman a yi adalci a kan yadda ake raba filaye da kuma daukar mataki kan matsalolin da sauyin yanayi yake haddasawa, da ma bai wa masu auren jinsi daya 'yanci.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A Nairobi, babban birnin Kenya, masu fafutika ne suka yi gangami domin tunawa da ranar Yaki da Talauci ta Duniya. Suna neman a yi adalci a kan yadda ake raba filaye da kuma daukar mataki kan matsalolin da sauyin yanayi yake haddasawa, da ma bai wa masu auren jinsi daya ‘yanci.

Kazalila mata na cikin wadanda suka fito kan titunan birnin Algiers na kasar Algeria ranar Talata, inda suka yi kira ga gwamnati ta sauka daga mulki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kazalila mata na cikin wadanda suka fito kan titunan birnin Algiers na kasar Algeria ranar Talata, inda suka yi kira ga gwamnati ta sauka daga mulki.

A ranar ce kuma, mambobin jam'iyyar hamayya ta Movement For Democratic Change (MDC) da ke Zimbabwe suka yi wani gangami a Harare. Makasudin yin gangamin nasu shi ne su sanya jam'iyyar a sabon tafarkin

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

A ranar ce kuma, mambobin jam’iyyar hamayya ta Movement For Democratic Change (MDC) da ke Zimbabwe suka yi wani gangami a Harare. Makasudin yin gangamin nasu shi ne su sanya jam’iyyar a sabon tafarkin “jajircewa wajen tabbatar da gaskiya da kyamar mulkin danniya”.

Presentational white space

Rakuma sun tsaya cirko-cirko ranar Asabar a yayin da wani dan kasuwar rakuma yake wucewa a cikin babbar kasuwar rakuma da ke birnin Nouakchott na kasar Mauritania...

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rakuma sun tsaya cirko-cirko ranar Asabar a yayin da wani dan kasuwar rakuma yake wucewa a cikin babbar kasuwar rakuma da ke birnin Nouakchott na kasar Mauritania…

Ranar Lahadi kuwa, wadannan 'yan dambe ne suka barje gumi a shahararren gefen tekun nan na Tergit da ke birnin.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ranar Lahadi kuwa, wadannan ‘yan dambe ne suka barje gumi a shahararren gefen tekun nan na Tergit da ke birnin.

Presentational white space

Ranar Litinin, wasu Kiristoci masu aikin ibada ne a Ethiopia suka shiga korama don yin wankan tsaki mai suna Fasilides a yayin da suke bikin Timkat. Ana yin bikin na Timkat domin tunawa da lokacin da aka yi wa Annabi Isa wankan baftisma a kogin Jordan.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ranar Litinin, wasu Kiristoci masu aikin ibada ne a Ethiopia suka shiga korama don yin wankan tsaki mai suna Fasilides a yayin da suke bikin Timkat. Ana yin bikin na Timkat domin tunawa da lokacin da aka yi wa Annabi Isa wankan baftisma a kogin Jordan.

A can kasar Kamaru kuma, wannan matar ce ke tafa wa masu tseren kekuna a lokacin da suka wuce ta garin NKoabang ranar Litinin a zagayen farko na gasar tseren kekuna ta La Tropicale Amissa Bongo tsakanin kungiyar Bitam da ke Gabon da takwararta ta Ebolowa da ke Kamaru.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A can kasar Kamaru kuma, wannan matar ce ke tafa wa masu tseren kekuna a lokacin da suka wuce ta garin NKoabang ranar Litinin a zagayen farko na gasar tseren kekuna ta La Tropicale Amissa Bongo tsakanin kungiyar Bitam da ke Gabon da takwararta ta Ebolowa da ke Kamaru.

A lesser flamingo sleeps with an eye open

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ranar Laraba, an hango wannan zalben yana bacci amma idonsa daya a bude a gidan ajiye namun dajin da ke birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu…

Washegari kuma, rana ce ta yi wa wannan mutumin da ke kwale-kwale zagi a tafkin Emmarentia Dam da ke tsakiyar birnin na Johannesburg. Masu koyon ninkaya na sha'awar zuwa wannan tafki domin yin atisayen gasar ninkaya.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Washegari kuma, rana ce ta yi wa wannan mutumin da ke kwale-kwale zagi a tafkin Emmarentia Dam da ke tsakiyar birnin na Johannesburg. Masu koyon ninkaya na sha’awar zuwa wannan tafki domin yin atisayen gasar ninkaya.

Presentational white space

An samu hotunan ne daga EPA da Getty Images

More from this stream

Recomended