
Fasinjoji bakwai ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru da safiyar jiya a kauyen Gada biyu dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Wani mazaunin Gada Biyu ya ce haɗarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na asuba kuma ya hada da mota kirar Sharon mai namba KFE 233ZF.
ya ce ana zargin motar tana tsaka da gudu ne ta kwace ta ci kwaro da wata babbar mota da ta lalace mai namba WAS 119 XA inda mutane bakwai suka mutun nan take.
Ya ce wasu fasinjojin sun makale cikin kangarwar motar har sai da jami’an hukumar FRSC mai lura da haɗura suka zo da inji suka cire su daga cikin motar da ta lallauye.
Da aka tuntubi kwamanda shiyar Abaji na hukumar FRSC,ACC Olasupo Esuruoso ya tabbatar da faruwar hatsarin da ya alakanta saba dokar gudu.