Madrid ta yi wasa 17 a jere ba a doke ta ba

Real Madrid

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Real Madrid ta fara shekarar 2020 da kafar dama, bayan da ta doke Sevilla 2-1 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu ranar Asabar.

Real wadda ta karbi bakuncin Sevilla a wasan mako na 20 a gasar ta La Liga, ta ci kwallaye biyu ta hannun Casemiro, yayin da Luuk de Jong ya ci wa Sevilla daya.

Da wannan nasarar Madrid ta yi wasa 17 a jere kenan ba a yi nasara a kanta ba, tun daga ranar 22 ga watan Oktoba a fafatawa da Galatasaray.

Karkashin koci Zinedine Zidane, Real ta yi wadan nan wasannin a gasar La Liga da Champions League da kuma Spanish Super Cup da ta lashe.

Kungiyoyin da Real ta kara da su a wasa 17 a jere da ba a yi nasara a kanta ba sun hada da Galatasaray haduwa biyu da Valencia ita ma fafatawa biyu.

Sauran sun hada da Leganes da Betis da Eibar da Real Sociedad da PSG da Alaves da Espanyol da Brugge da Barcelona da Athletic da Getafe da Atletico da kuma Sevilla.

Kalubalen da ke gaban Real Madrid shi ne Copa del Rey da za ta ziyarci Unionistas de Salamanca ranar Laraba.

Haka kuma Real za ta yi gumurzu da Real Valladolid a gasar La Liga ranar Lahadi karawar mako na 21.

More from this stream

Recomended