Plateau United ta caskara Adamawa United | BBC Hausa

Nigerian Premier League

Hakkin mallakar hoto
Npfl

Plateau United ta dare mataki na daya a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya, bayan da ta casa Adamawa United.

Plateau United ta doke Adamawa United da ci 5-0 a wasan mako na 16 da suka fafata ranar Lahadi.

Mai masaukin baki ta ci kwallayen ne ta hannun Oche Ochowechi da Uche Onwuasoanya da Abba Umar da kuma Ibrahim Mustapha wanda ya zura biyu a raga.

Da wannan sakamakon Plateau ta hada maki 28 kenan, ita kuwa Adamawa United ita ce ta karshen teburi da maki 11.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga:

Lobi 0-0 Dakkada

  • Heartland 0-0 Katsina United
  • Rangers 3-1 Abia Warriors
  • FC Ifeanyiubah 2-0 Enyimba
  • Kano Pillars 2-0 Akwa United
  • Kwara United 0-0 Sunshine Stars
  • Wikki 2-1 MFM

Sai a ranar Litinin za a karkare wasa daya, inda Jigawa Golden Stars za ta karbi bakuncin Rivers United.

Jigawa tana ta 19 a kasan teburi da maki 13 da kwantan wasa daya, Rivers kuwa ita ce ta uku a saman teburi da maki 27.

Haka kuma Nasarawa United za ta karbi bakuncin Warri Wolves.

Nasarawa tana ta 18 mai maki 14, yayin da Warri Wolves take ta 15 da maki 18.

More from this stream

Recomended