Tankar mai ta kama da wuta a Anacha – AREWA News

Wata motar tanka kirar Mack dake makare da man fetur da aka ajiyeta akan hanyar Anacha zuwa Awka ta kama da wuta da safiyar ranar Litinin.

Ana tunanin wutar ta samo asali ne sakamakon tartsatsin wuta daga batirin motar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,SP Haruna Muhammad cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce lamarin ya faru ne da karfe biyu na dare lokacin da aka ajiye motar a wajen gidan man Vin Oil.

Ya ce bayan samun kiran kai daukin gaggawa tawagar yansanda dake aikin sinitiri a karkashin jagorancin baturen yansanda na Awada sun garzaya wurin inda suka gaggauta kiran hukumar kashe gobara ta jihar kuma sukai gaggawar amsa kiran.

More from this stream

Recomended