Damben Garkuwa da Kanin Bello ya yi kwantai

Garkuwa Kanin Bello

Damben Garkuwan Cindo da Ali Kanin Bello ya ci karo da cikas a dambatar da suka yi ranar Lahadi da safe.

Tun farko Ali Zuma, shugaban kungiyar dambe ta kasa reshen babban birnin tarayya ne ya sa musu damben mota ga Zakara da naira dubu 100 ga duk wanda aka buge.

Tun kan dambatawar Ali Zuma ya bayar da sanarwar dokokin damben, domin ‘yan kallo su san yadda za a gabatar da wasan

Kafin ‘yan wasan su kara Garkuwan Cindo ya buge Ali Kanin Bello sau uku a tarihi, saboda haka Ali ya dauki damben da mahimmaci.

Wasan ya kayatar an kuma yi damben da kowa sai da ya gaji, sai dai a kwai lokacin da Ali Kanin Bello ya kwance hannu aka ba shi minti biyu idan bai dawo ba an cire shi.

Can kuma sai Ali Zuma ya ce m,inti 10 da zarar Ali Kanin Bello bai koma dambe ba za a bai wa Garkuwa mota.

Ali Kanin Bello ya samu damar hutun da ya koma damben, inda suka ji wa juna ciwao, shi garkuwa ya ji ciwo a kulle, Ali kuma a fuska.

Haka suka ci gaba da dambe sai da tai cewar suna klasa dukan junansu, amma dai Garkuwa ya fi Ali Kanin Bello kuzari.

Kanin Bello ya samu damar makin buge Garkuwan Cindo, inda ya dunga dukansa a daf da layi, amma ina sai kaga Garkuwa a tsaye kamar ba shi ake duka ba.

Haka aka ci gaba ana dambe ana hutawa har ta kai Ali Kanin Bello ya gaji likis, amma yana cikin fili, hakan ya sa aka je hutu, tun daga nan ba a koma ba, amma jikin Garkuwa da laka yana zagaya fili.

Da haka ne ‘yan kallo suka bukaci da a bai wa Ali Kanin Bello loklaci idan bai dawo ba a bai wa Garkuwa mota.

Haka dai fili ya rude kowa na fadin albarkacin bakinsa kan abin da ya kamata ayi.

Yanzu dai an cimma matsaya za a koma damben da yammaci, inda za a yi turmi uku.

Kowanne turmi minti uku sannan ayi hutun minti daya, turmin farko dana biyu, babu kidayar maki.

Amma za a duba wanda yafi duka a turmi na uku idan ba ta yi kisa ba sai a ba shi mota.

Related Articles