
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Bayan da aka raba jadawalin gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League ranar Litinin, Real ta maida hankalin kan tunkarar fafatawa da Barcelona.
A ranar Laraba ne Real Madrid za ta ziyarci Camp Nou domin buga wasan hamayya da ake kira El Clasico a gasar cin kofin La Liga.
‘Yan wasan Real Madrid da suka hada da Marcelo da Hazard da James da Lucas Vázquez da kuma Asensio sun yi atisaye a kokarin da suke yi na murmurewa daga rauni.
Cikin atisayen da Real Madrid ta yi ranar Litinin ta gayyaci matasan ‘yan wasanta shida da suka hada da Altube da Manu Hernando da Ayoub da Blanco da Rodrigo da kuma Miguel.
Tun farko an tsara fafatawa tsakanin Barcelona da Real Madrid ranar 26 ga watan Oktoba, amma zanga-zanga da aka yi a Catalunya ya sa aka dage wasan.
Bayan da suka buga wasa 16 a gasar La Liga ta bana, Barcelona da Real Madrid suna da maki iri daya 35.
Sai dai Barcelona ce ta daya a kan teburi, sai Real Madrid ta biyu, wadda aka bai wa tazarar kwallaye biyu tsakaninta da Barca.
Real Madrid za ta kara da Manchester City a gasar cin kofin Zakarun Turai ranar 26 ga watan Fabrairun 2020, ita kuwa Barcelona za ta ziyarci Napoli kwana daya kan wasan Real.