An tsare matar mataimakin shugaban Zimbabwe saboda rashawa

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ministan kudin Zimbabwe Mthuli Ncube a lokacin da ya isa majalisa domin gabatar da kasafin kudin kasar kwanaki kadan bayan fitar da sabuwar takar dar kudu a ranar 14 ga watan Nuwamba 2019

Matar mataimakin shugaban kasar Zimbabwe Constantino Chiwenga, na hannun jami’an tsaro saboda zarginta ta ta’ammuli da haramtattun kudaden kasashe waje.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawar kasar ta ce an tsare Marry Mubaiwa ne a yammacin Asabar. Gobe Litinin ne ake sa ran gurfanar da ita a gaban kotu.

Tuhumar da ake wa Marry ta hada da batun sayen motocin alfarma guda biyu da ta yi a Afirka ta Kudu.

Rahotanni na cewa Marry na bin wata kazamar hanyar neman rabuwa da mijinta, wanda aka jima ana ganinsa a matsayin babbar barazana ga shugaba Emmerson Mnangagwa a siyasance.

Shugaba Mnangagwa na fuskantar karin matsin lamba a kan matsalar tattalin arzikin kasar, kuma ya yi alkawarin magance matsalar cin hanci da rashawa.

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) Æ™arÆ™ashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da Æ™arar da É—an majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]