
Hakkin mallakar hoto
AFP PHOTO/KCNA VIA KNS
Shugana Kim Jong-un ya kara irin barazanar da yake wa Amurka a ‘yan kwanakin nan.
Koriya ta Arewa ta sake gudanar da wani ‘muhimmin’ gwajain makamai a karo biyu cikin mako guda, domin kara karfin nukiyilar kasar.
Wani kakakin ma’aikatar Nukiliyar Koriya ta Arewa ya tabbatar da gwajin Nukiliar da aka yi a ranar Juma’a. Sai dai jami’in bai yi karin bayani ba, a cewar kamfanin dillacin labarin kasar KNCA.
Karo na biyu ke nan da kasar ke gudanar da gwajin Nukilya a cikin mako guda, yayin da kasar da kuma Amurka ke tattaunawa game da dakatar da shirin Nukiliyar Koriya ta Arewar.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ki amincewa da janye tsattsauran takunkumin da kasarsa ta sa wa Koriya ta Arewa ta yi watsi da shirinta na Nukiliya.
Maimakon haka, sai shugaba Kim Jong-un ya kara neman gwamnatin Amurka ta janye wasu sharuda da bukatun da ta gabatar.
Koriya ta Arewa ta ce idan ba ta samu hakan ba, to za ta yi amfani da “sabbin hanyoyi”. Ta kara cewa idan Amurka ta ki, to ta kwana da shirin samun wani mugun kyauta da Kirsimeti.
Mene ne gwajin?
Babu tabbaci game da irin makamin da Koriya ta Arewa ta harba.
Wani kwararre kan Koriya ta Arewa a Cibiyar kimiyya ta Amurka Ankit Panda, ya ce akwai yiwuwar gwajin na makamin mai linzami mai ‘ya’ya ne.
A baya ministan tsaron Koriya ta Kudu ya ce akwai yiwuwar makwabciyar ta su za ta yi gwajin makamin mai linzami mai ‘ya’ya.
A baya dai Koriya ta Arewa ta ce za ta rufe tashar gwajin Nukiliyarta na Sohae.