Arsenal ta ci wasa daya cikin 10 da ta buga | BBC Sport

Gabriel Martinelli

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matashin dan wasa Gabriel Martinelli mai shekaru 18 mafi karancin shekaru da ya ci wa Arsenal kwallo a bana

Kocin rikon kwaryar Arsenal, Freddie Ljungberg ya samu nasarar cin wasa a karon farko tun bayan karbar jagorancin kungiyar.

Sai yanzu Arsenal ta ci wasa daya cikin wasa goma da ta buga a baya-bayan nan, a wasan hamayyar London da ta buga da West Ham a ranar Litinin.

Angelo Ogbonna ne ya fara jefa kwallon farko a ragar Arsenal a minti na 38 da fara wasan, a filin wasan na London.

Matashin dan wasa Gabriel Martinelli mai shekara 18 wanda ya fara buga cikakken wasa a Premier ne ya zare kwallon da aka zira wa Arsenal, a minti na 60.

  • Ingila za ta kara da Italiya a wasan sada zumunci
  • An haramta wa Rasha wasanni har shekara hudu

Cikin minti kasa tara da farke kwallon, Niclos Pepe ya kara kwallo ta biyu yayin da Pierre-Emerick Aubameyang ya kara ta uku a wasan, kuma ta 11 a kakar ta bana.

Rashin nasarar tasa an kara matsin lamba ga mai horas da West Ham din Manuel Pellegrini, wanda maki hudu kawai ya samu cikin wasa tara da ya buga a Premier.

Yanzu West Ham na matsayi na 16 wato matsayi daya ne tsakaninta da kungiyoyi ukun karshen teburi, kuma za ta buga wasanta na gaba ne da Southampton a ranar Asabar.

Yanzu dai Arsenal ta haura sama da mataki biyu kacal, inda take a matsayi na tara, da kuma maki 24 tsakaninta da Liverpool da ke matsayi na daya a Premier.

More from this stream

Recomended