Ganduje ya nada Sarkin Kano Shugaban majalisar Sarakunan jihar shugaba

Gwamna Ganduje da Sarki Sanunsi

Gwamnan jihar kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar.

A wata sanarwa da babban sakataren hulda da ‘yan jaridu na gwamnan, Abba Anwar, ya fitar a tsakar daren da ya gabata, ya ce, bisa tanadin sashe na 4 (2) (g) da sashe 5 (1) (2) na dokar masarautun jihar ta 2019, gwamnan jihar ya nada, Alhaji Muhammadu Sanusi na II, Sarkin Kano a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan.

Sanarwar ta kara da bayyana cewa daga cikin sauran ‘yan majalisar akwai dukkanin sauran sarakunan jihar masu daraja ta daya, na Bichi da Rano da Karaye da Gaya, Alhaji Aminu Ado Bayero, Alhaji Dr Tafida Abubakar (Autan Bawo), Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II da kuma Alhaji Ibrahim Abdulkadir.

Haka kuma sanarwar ta kara da cewa sashe 4 (2) na dokar ya ba wa Sakataren gwamntaiin jihar da kwamishinan kananan hukumomi da shugabanin kananan hukumomi dai-dai daga kowace daya daga cikin masarautun biyar damar zama mambobi.

Akwai kuma akalla masu nada sarki goma, akalla biyu daga kowace masarauta daga cikin su biyar din, haka kuma da babban limamin kowacce daga cikin masarautun.

Nadin ya kuma hada da wasu wakilai na ‘yan kasuwa daga masarautun da kuma wakilai na hukumomin tsaro. Sannan kuma shugabancin kamar yadda sanarwar ta bayyana zai zama na karba-karba.

More from this stream

Recomended