Kotu ta ba da umarnin kai El-Zakzaky da matarsa gidan yari

zakzaky

Wata kotu da ke zama a Kaduna ta yanke hukuncin mayar da jagoran kungiyar IMN a Najeriya Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa gidan yari daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis da safe, inda ta ce za a mayar da su gidan yarin ne don lauyoyinsu da likitocinsu su samu damar ganinsu cikin sauki.

Tun watan Disambar shekarar 2015 gwamnatin Najeriya ke tsare da malamin biyo bayan rikicin da ya faru tsakanin mabiyansa da jam’ian tsaro a Zariya.

Alkalin Mai Shari’a Gideon Kudafa ya daga ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa 9 ga watan Fabrairun 2020.

A watan Maris ne Mai Shari’a Gideon Kudafa ya daga sauraren karar har sai baba ta gani sakamakon sanya shi cikin mambobin kotun sauraron kararrakin zabe.

More from this stream

Recomended