Sarkin Hausawan Turai, Alh Sirajo Jan Kado ya nada hakimai takwas a masarautarsa da ke Paris
Sarkin Hausawan Turai tare da Marafan Hausawa kuma Hakimin London, Alhaji Muhammadu Sanusi da kuma Dan Isa, Dr Usman T Shehu
Hakimai takwas Sarki Jan Kado ya nada a ranar Asabar a fadarsa da ke Paris
Wadanda aka nada sun fito daga kasashe daban-daban na Turai
Sarki Jan Kado Na kokarin raya al’adun Hausawa a Turai
Akwai masu rike da sarautar Dan buran, da Sallama, Da Falaki da Shamaki da kuma Uban Doma
Masarautar na da Jakadiyar Sarki, da Giwar Sarki da kuma Gimbiyar Mawaka
An baiwa Fati Nijar sarautar Gimbiyar Mawakan Hausawan Turai
Baya ga wadanda aka nada sarautar, wasu sun halarci bikin nadin daga kasashe daban-daban na nahiyar Turai
An nada Jakadiya da kuma Giwar sarki
Masu rike da sarauta a masarautar kan sanya kaya irin na al’adar kowace masarauta da ke kasar Hausa
Wadanda aka nada wa sarauta sun hada da mata da maza daga yankuna daban-daban
Sarki Jan Kado Na kokarin raya al’adun Hausawa a Turai
A makonnin baya, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci masarautar a Paris inda ya jadadda sarautar Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Surajo Jan Kado
Daya daga cikin kofofin shiga fadar sarkin Hausawan Turai da ke Paris a kasar Faransa.