Firimiya Lik: Mourinho ya ci wasansa na farko

Jose Mourinho

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasan farko kenan da Jose Mourinho ya jagoranta tun bayan da ya karbi ragamar Spurs

Mourinho ya ci wasansa na farko da ya ja ragama a Premier bayan kusan shekara daya, inda wasa ya tashi 3-2 sakamakon kokarin zaratan ‘yan wasa Son da Harry Kane.

Jose Mourinho ya ci dukkanin wasanni 36 da ya buga wadanda a cikinsu ya fara zira kwallo biyu ko fiye da haka a raga, yau kuma ya ci na 37.

Har bayan minti 70 na wasan West Ham ba ta nuna za ta yi wani katabus ba sai da Antonio ya farke guda daya a minti na 74.

Son Hueung-min ne ya fara jefa kwallo a ragar West Ham cikin minti na 36 bayan ya ja kwallo cikin raga ta bangaren hagu, inda ya shauda ta da kafar hagun.

Sai kuma a minti na 43 da Son din ya taimaka wa Lucas Moura ya ci ta biyu, minti biyar bayan haka kuma Harry Kane ya kara ta uku.

Son ya ci wa Tottenham kwallaye mafi yawa a kowacce gasa sama da kowanne dan wasa a shekarar 2019, inda ya ci 18 – kwallo daya kenan tsiransa da Harry Kane.

Shi kuwa Harry Kane ya shiga jerin ‘yan wasan da suka fi ci wa Tottenham kwallaye a tarihin kungiyar. Yanzu yana da kwallo 175, inda yake bin bayan Jimmy Greaves da ke da kwallo 266 da kuma Bobby Smith me 208.

Ogbonna ne ya farke ta biyu a mintin karshe bayan an kara minti shida, abin da ya kada hantar Tottenham.

Sakamakon ya sa Tottenham ta koma matsayi na shida amma wasannin da za a yi na gaba ka iya sauya mata zama a teburin.

More from this stream

Recomended