Najeriya da Afrika ta kudu sun amince su ba wa ‘yan kasar bizar shekara 10 |BBC Hausa

uhammadu Buhari da Cyril Ramaphosa

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da Cyril Ramaphosa na Afirka ta kudu

Afirka ta kudu da Najeriya sun amince kan bai wa ‘yan kasuwa da malaman makarantu da masu zuwa kasar akai-akai takardar izinin shiga kasashen, biza mai wa’adin shekara 10.

An cimma wannan yarjejeniya ne bayan kammala taron hukumar hadin gwiwa tsakanin Afirka ta kudun da Najeriyar karo na tara da aka gudanar a Pretoria, babban birnin kasar wanda shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da takwaransa na Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa suka jagoranta.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan kafafen yada labarai, Garba Shehu ya fitar ta ce wannan ne karon farko da shugabannin suke jagorantar irin wannan taro tun bayan samar da hukumar hadin gwiwar tsakanin kasashen biyu.

An dai dauki matakin ne domin inganta alaka tsakanin al’ummomin kasashen biyu da habaka tattalin arzikinsu da al’ada da harkokin siyasarsu, bayan hare-haren kin jinin baki ‘yan waje ciki har da ‘yan Najeriya da aka yi a Afirka ta Kudu.

A taron da aka gudanar a fadar shugaban Afirka ta kudu, shugabannin biyu sun amince da daukar matakin riga-kafi kan rikici kafin ya ta’azzara da bukatar musayen bayanan sirri da nufin karfafa kawancensu na tsaro.

Kasashen biyu sun kuma yanke shawarar samar da wani taro da wakilan gwamnatocin za su rika ganawa lokaci zuwa lokaci kamar sau biyu a shekara domin tattauna batutuwan da suka shafi walwalar jama’arsu.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama da takwaransa na Afirka ta kudu, Dakta Naledi Pandor su ne suka rattaba hannu kan takardar da ke kunshe da batutuwan da aka tattauna a taron.

More from this stream

Recomended