‘Gwamnati na yunkurin musanya Sarkin Kano da na Bichi’ | BBC Hausa

Mallam Muhammadu Sunusi II

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II

Wata kungiya da ke cewa ta dattawan Kano ce ta ce ta samu labarin gwamnatin jihar na shirin mayar da Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sunusi II masarauta Bichi, na Bichin kuma Aminu Ado Bayero ta dawo da shi Kano.

Jami’i a kungiyar, Kwamared Ibrahim Wayya wanda ya yi Allad-wadai da matakin, ya bayyana wa BBC hakan ne inda ya ce sun dauki matakin bayyana ra’ayinsu kan batun domin ankarar da gwamnatin tarayya da al’umma kan labarin take-taken gwamnatin Kano da suka samu na dauke Sarkin Kano daga masarautarsa zuwa masarautar Bichi.

Kwamared Wayya ya ce har yanzu kungiyarsu ba ta yarda da masarautun yanka hudu da gwamnatin Kano ta kara ba inda ya ce masarautar da suka sani ita ce wadda Sarki Sunusi II ya ke jagorantarta.

A cewar Ibrahim Wayya, ”tun da batun yana gaban kotu, babu mai tursasa musu amincewa da fadada masarautar.”

Sai dai gwamnatin Kano ta bakin sakataren yada labaranta, Abba Anwar, ta magantu kan zargin ita kungiyar in da ta ce, ”kawai kururuwa kungiyar take yi sannan bayanan da ta yi, ba su da tushe balle makama.”

A kwanakin baya ne dai wasu hotunan sabbin sarakunan da aka manna a saman bangon dakin taro na mika sandar mulki (Coronation Hall) da ke fadar gwamnatin Kano wanda aka sa ka hoton Sarki Sunusi a karshe bayan na sabbin sarakunan ya janyo cece-kuce abinda masu tsokaci kan al’amuran yau da kullum su ke kallon har yanzu tsugunu ba ta kare ba kan batun ko da ya ke Abba Anwar din bai ce komai ba kan wannan batun.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A watan Mayun bana ne gwamnatin Kano ta kirkiri sababbin masarautu hudu a Kano

Dangantaka a tsakanin bangarorin biyu na ci gaba da yin tsami tun lokacin da Gwamna Ganduje ya kirkiri sabbin masarautu 4 a jahar, matakin da ake zargin cewa ya dauka ne domin rage karfin ikon Sarkin Kano, duk kuwa da cewa ya musanta.

More from this stream

Recomended