Majalisar zartarwar jihar Kaduna ta amince da fara biyan mafi karancin albashi da kuma karin albashi ga ma’aikatan daga daga daya ga watan Satumbar 2019.
A wata sanarwa mai dauke da sahannun Muyiwa Adekeye ma shawarcin gwamnan jihar na musamman kan harkokin sadarwa ya ce taron majalisar ya guda na ne karkashin jagorancin mataimakiyar gwamnan jihar, Dr . Hadiza Balarabe.
Ya lura cewa hakan na daga cikin kokarin gwamna Nasir El-Rufai na bunkasa aikin gwamnati.
Aiwatar da sabon tsarin albashin na nufin masu daukan mafi ƙarancin albashi a jihar za su samu karin kaso 67 ya yin da wadanda suke matakin albashi daga na 10-14 za su samun karin kaso 60.
Hakan na nufin kudin da jihar za ta rika kashewa wajen biyan albashi a kowanne wata zai karu da naira biliyan guda daga biliyan ₦2.827 zuwa biliyan ₦3.759.