Ko masinja bai kamata Buhari ya ba Sabo Nanono ba – Dan Bilki Kwamanda

A wani shirin siyasa na gidan rediyon Rahma a jihar Kano, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda wanda Dan-a-mutun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ragargaji Sabo Nanono da Buhari ya mika sunansa a jerin sabbin Ministoci.

A cewar Kwamanda Sabo Nanono mutum ne da bai cancanci a ba shi amana ba, saboda kasancewar an san halinsa tun daga kan Bankin Arewa (Bank Of The North) Kana kuma wanda suka ci moriyar farin jinin Buhari don biyan bukatun kansu.

Kwamanda ya jaddada cewa zai je Abuja domin ganawa da Buhari don ba shi shawarar janye wannan kudiri na ba Nanono Minista.

“Na fada na kuma fada bai dace da wannan mukami ba”. Ya jaddada.

More from this stream

Recomended