HomeMoreYaron da aka sace don ya zama dan jagora a Najeriya |...

Yaron da aka sace don ya zama dan jagora a Najeriya | BBC Hausa

Published on

spot_img

Samuel Abdulraheem ba ya tuna ranar da aka sace shi yana da shekara bakwai daga gidan iyayensa a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.

Duk da cewa ya fito ne daga gida mai yawan mutane- mahaifinsa na da yara 17 da mata hudu- an bar Samuel da mai rainonsa su kadai a gida ranar.

An shaida wa ‘yan gidansu ya fita waje ne don ya tuka kekensa.

Ashe ba za su sake ganinsa ba sai bayan shekara shida.

Allura cikin ruwa

“Babu abin da ba mu yi ba don mu gano shi.” in ji yayarsa Firdausi Okezie.

Lokacin tana da shekara 21, ba a bayyana mata ya bace ba.

Dama dai kanin nata na kaunar rugawa ya dauki waya duk lokacin da ta bugo wayar daga jami’a.

Don haka, da ta lura cewa sauran ‘yan gidansu ne ke daukar wayar idan ta bugo, sai jikinta ya bata cewa wani abu ya faru.

Bayan da ta gama darasi wani yammaci, sai Firdausi ta kama hanyar gida. Dole mahaifinta ya bayyana mata abin tashin hankalin da ya faru: Dan uwanta da ta fi so ya bata fiye da tsawon wata guda.

Hakkin mallakar hoto
Abdulraheem family

Image caption

Da farko ba a shaida wa mahaifiyar Samuel batun bacewarsa ba

“Da farko, babana ya sa an kama mai rainon amma da aka yi bincike sai aka sake ta,” in ji Firdausi.

Haka kuma, an yi kokarin boye wa mahaifiyar Samuel wacce ba ta tare da mahaifinsa da dadewa. Duk lokacin da ta kira waya daga gida da take aure a wani garin, sai a kirkiri wani abu a gaya mata.

Daga baya sai aka yanke shawarar tura wani kawunsa ya fada mata abin da ya faru.

Baya ga bincike mai zurfi da ‘yan sanda suka yi, an buga hotunansa a jaridu sannan an yi ta nemansa a tituna daban-daban. An duba ramuka ko da mota ce ta bankade shi. Har da malamai aka bi don nemansa.

A hankali, mahaifinsu ya nemi duka mutanen gidan su sa a ransu cewa dan uwansu ya mutu- sun yi dukkan mai yiwuwa.

Firdausi dai ba ta hakura ba. Ta sadaukar da makalarta ta kammala jami’a kan kaninta da ya bace kuma shekara guda da gama jami’a ta koma Legas don neman aiki.

Ta koma addinin Kirista kuma ta fara zuwa cocin Winners Chapel- daya daga cikin manyan coci-coci dake Najeriya.

Ko wane watan Disamba, cocin na taron addu’o’i na kwana biyar.

A lokacin wannan taron wanda aka fi sani da Shiloh, ana bai wa mambobin cocin rumfuna kyauta don baje hajarsu a harabar cocin.

Har a lokacin, Firdausi ba ta samu aiki ba, sai ta nemi a bata rumfa don ta baza zanin kamfala da mahaifiyarta ta yi.

Yayin da take jira kafinta ya kafa mata rumfar, sai ta zauna a kan wata kujera ta dora kanta a kan cinyarta don ta dan huta.

A lokacin ne ta ji wani mai mutum yana bara, a ba shi sulalla.

Mai barar ya dafa hannunsa a kafadar wani yaro ta hagu, kuma yaron na sanye ne cikin riga ruwan kasa da wandon da yayi masa kadan duk sun fatattake.

Firdausi ta yi kara- dan jagoran dai ba wani ba ne illa kaninta ne da ya bata.

Yadda aka sace shi

Samuel, wanda yanzu ya jke da shekaru 30 ya ce ba ya tuna yadda aka sace shi daga gidansu: “Abin kawai da anke tunawa shi ne tafiyar da muka yi a jirgin kasa.”

An kai shi wurin wata mata da ke zaune a wajen Legas a wata unguwa wacce mafi yawa masu nakasa kuma mabarata ke zama a cikinta.

Matar ta rinka bayar da hayansa ga makafi mabarata kan naira 500 kullum.

Samuel ne kawai ya zauna da matar, inda ya rinka kwana a kan tabarma a dakinta da aka yi da katako.

Cikin shekarun da ya yi , ya ce kusan yara maza biyar ne suka zo zama da sauran matan dake kusa su kuma ko wannensu ana bayar da shi haya ga mabarata.

Samuel ya yi tunanin an yi masa wani abu ko kuma an ba shi wani abu ya ci ko kuma ya sha a lokacin saboda ba ya tunanin ‘yan gidansu a lokacin, ko kuma tunanin halin da suke ciki.

“Ba na jin ina da tausayi a loacin,” a cewarsa. “Kawai dai kamar fatalwa nake sai dai in je in yi aikin dan jagora. In samo kudi, in ci abinci in yi bacci, gobe ma haka.

Rayuwar bauta

Mabarata daban-daban sun rinka hayarsa tsawon lokaci kama daga sati guda zuwa wata guda.

Idan dare ya yi kullum, sai Samuel da mabaracin su yi bacci tare da sauran mabarata a gefen tituna.

Idan mabaracin ya ji dadin aiki da shi, sai ya sake yin hayarsa tsawon wani lokacin.

“Na zama kamar bawa, ” ya ce. “Ban isa in ce zan je wani wuri ba ko kuma zan yi wani abu ba. Dole in zama ina kusa a ko da yaushe.

Da yake kullum a tafe yake, sai Samuel ya yi ‘yan abokai inda wani lokaci ya kan yi wasa da ‘ya’yan wasu mabaratan da yamma.

Wani lokaci mutane kan basu abinci idan suka yi bara. A wasu lokutan kuwa sai su tsaya a gaban gidajen abinci su ci ragowar na mutane ko su diba a bola.

“Kullum ina cikin yunwa. Da rana idan una aiki, da wuya in samu damar zama in ci abinci.” ya ce.

“Ina ganin mabaratan ba mutanen banza bane. Suna tashi daga bacci, su yi bara yadda mutane ke tashi da safe su tafi aiki.”

Kullum Samuel na takawa daga wani yankin na Legas zuwa wani a matsayin dan jagora.

Wani lokaci su kan taka zuwa wasu jihohin dake makwaftaka ko kuma su tsallaka Jamhuriyar Benin. Idan mabaratan suka samu labarin wasu masu karziki za su yi taro a wani waje, sai su gaya wa Samuel ya kai su wajen da motar Bas.

“Akwai lokutan da na ke gajiya sai in ki tsayawa don mu yi bara amma makafi na da saurin gano abu- jinsu na da kaifi. Wani lokaci sai su karkatar da kafadata su ce ‘Akwai wani a nan. Me ya sa ka wuce shi?’

Abin al’ajabi ya faru

A watan Disambar 2000, wani mabaraci da yake yi wa dan jagora ya ji labarin taron da ake yi a cocin Winners Chapel inda suka gamu da yayarsa.

Da farko, Firdausi ta kidime ta kasa mika hannu ta taba kaninta- wanda har yanzu bai manta ihun da ta yi ba.

“Sai na fadi a kasa,” ta ce.

Samuel ya rame, kafadarsa ta dama ta karkace kuma ya yi dif kamar kurma, ba ya cewa uffan. Ganin haka Firdausi ta fashe da kuka.

“Na dan jima ban gane ta ba, duk da na ga alamar sanayya- alamar cewa wannan ‘yar uwata ce,” in ji Samuel.

Hakkin mallakar hoto
@davidoyedepoministries

Image caption

Shugaban cocin Winners Chapel David Oyedepo

Nan da nan aka taru kuma ma’aikatan cocin ma suka iso. Suka yi kokarin fahimtar abin da Firdausi ke cewa.

Suka ja Samuel gefe suka yi masa wanka. Aka ba shi wankakkun kaya ya sa sannan aka dora shi da yayarsa kan dandamalin coci kuma aka bai wa Firdausi lasifika.

Cikin kuka ta bayyana yadda ta gano kaninta wanda ya kwashe tsawon shekaru shida a bace.

Taron ‘yan cocin suka rika jinjina tare da godiya ga Allah.

A wannan daren sun kwana a harabar cocin a cikin mota, saboda hanyar inda Firdausi take zama da nisa.

Ta rinka tashi cikin dare tana taba kaninta don tabbatar da cewa shi din ne.

Samuel ya bayyana cewa daf da zai gamu da yayarsa, an kai wani sabon yaro gidan matar.

Da farko, yaron ya yi ta kuka ba kakkautawa kuma ya ki cin abinci. Nan da nan, sai ya daina kukan kuma haka ya sa Samuel zargin cewa an yi masa wani abu ne don a karkatar da hankalinsa daga tunanin gida.

Hakkin mallakar hoto
Firdausi Okezie

Image caption

Samuel da yayarsa ranar aurenta, kusan shekaru biyu bayan da ta gano shi

“A kasar da ta ci gaba sai ka je ka gaya wa ‘yan sanda. Amma a nan, ‘yan sanda za su ce ka ba su kudin man mota da sauransu kuma a lokacin ma ni bana aiki,” in ji Firdausi.

Kuma baya ga haka ma, gyara rayuwar kaninta wanda ya ke da shekara 13 a lokacin shi ya fi ba ta wahala. Bai koma wajen mahaifinsu ba sai ya ci gaba da zama da ita tana kula da shi.

Duk jikinsa kuraje ne masu tsananin wari.

Kafadarsa ta dama ta dade a karkace, sai da a ka rika kai shi asibiti ana ba shi magunguna kafin ta dawo dai-dai kuma ta daina nuna matsin da ta shiga na damkar da mabarata ke mata.

Mahaifiyarsu ba ta gane dan autanta ba- wanda a yanzu ya lalace, ya kazance.

Sai da ta daga hannunsa ta duba wata tawadar Allah sannan ta amince mutumin da ke gabanta danta ne na cikinta.

Dalibi

Bayan shekara 6 ba ya zuwa makaranta, Samuel bai iya rubutu da karatu ba.

Firdausi ta kai shi makaranta amma sai aka ce ai ya tsufa da makarantar firamare.

Sai ta hadu da wata mata mai makaranta kuma ta maince ta sa shi a makarantarta yayin da Firdausi ta shirya samar masa malamin da zai rika yi masa karatu idan ya taso daga makaranta.

Hakkin mallakar hoto
Samuel Abdulraheem

Image caption

Samuel ya zama mai hazaka a makaranta

Ya ci duka jarabawarsa sosai kuma a lokacin da ya kai shekara 17 sai ya zana jarabawar shiga jami’a.

Nan ma ya ci fiye da yadda ake tsammani don kuwa shi ya zo na daya a makarantarsu gaba daya kuma ya samu Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya karanata fannin Injiniya.

Sai dai kwazonsa da hazakarsa ta jefa shi cikin matsalar da ta kawo karshen karatunsa.

Sauran dalibai na zuwa wajensa don neman taimako a fannin karatu kuma a shekararsa ta hudu a jamai’a aka kama shi yana rubuta wa wani dalibi jarabawa.

Yanzu Samuel na aiki ne a filayen da ake gini a kansu a matsayin mai kula da ayyuka.

“Wata rana idan na samu wadata, ina da burin in ci gaba da karatu na,” ya ce. Ya kara da cewa watakil ya karanci kimiyyar komfuta tunda ya iya sarrafa komfuta da makamantanta.

Samuel ya ce ba ya bakin ciki da halin da ya shiga a baya. Yana ganin cewa rayuwar da yayi ta taimaka masa zama mutum mai kirki.

“Bana taba jin haushin mutane ko in riki wani a zuciyata,” ya ce.

Samuel ya ce yana fatan cewa labarinsa zai karkatar da hankalin mutane kan mabarata da ‘yan jagorarsu.

“Idan suka ga mabaraci da dan jagora, su yi nazari a kan cewa babu mamaki yaron nan na bukatar taimako,” a cewarsa. “Kada kawai ku mika kudi ku tafi.”

Ma’aikaciyar BBC Manuella Bonomi ce ta yi zanen

Fassarar Fauziyya Kabir Tukur

Latest articles

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin...

More like this

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...