Wasu yanbindiga da safiyar ranar Litinin sun far wa makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Plateau inda suka saci mutum daya.
Maharan sun kai farmaki ne kan rukunin gidajen malamai na makarantar dake Heipang a karamar hukumar Barikin Ladi dake jihar.
Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar,Tyopev Terna ya tabbatarwa da jaridar The Cable faruwar lamarin.
Matar da aka sace mai shekaru 24 kanwace ga Ezekiel Rangs mataimakin magatakaradan makarantar.
Harin shine na biyo kan makarantar cikin watanni biyu bayan makamancinsa da aka kai cikin watan Faburairu inda aka sace wani Yaro dan shekara 12.